'Yan fashi sun yi awon gaba da miliyoyi a ofishin MTN

'Yan fashi sun yi awon gaba da miliyoyi a ofishin MTN

Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da kutsen da wasu 'yan fashi da makami suka yi a ofishin MTN da ke yankin Tudun Wada na Birnin Kebbi. Kakakin rundunar, DSP Nafi'u Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Alhamis.

"Tabbas, anyi fashi da makami kuma an fara bincike," in ji shi.

Tun farko dai, Alhaji Ibrahim Dasuki, manajan MTN na jihar ya sanarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa 'yan fashin sun kutsa ofishinsu da ke Tudun Wada wajen karfe biyu na ranar Laraba. Sun yi awon gaba da kudi har naira miliyan hudu da rabi.

"Yan fashin sun yi wannan aika-aikar ne a cikin mintocin da basu wuce biyar ba kuma sun iso ofishin ne wajen karfe biyun rana. Sun kwashe kudi har naira miliyan hudu da rabi," in ji shi.

Ya yi bayanin cewa maza uku ne suka je ofishin da fuska a rufe kuma a wata mota kirar Toyota Saloon mai lambar jihar Bauchi.

DUBA WANNAN: Kungiyar Shi'a tayi magana a kan jita-jitar mutuwar Zakzaky

"Bayan isarsu ne 'yan fashin suka fito da bindigogi kirar AK 47 kuma suka umarci mutanen da ke wajen ofishin da su kwanta kasa."

Ya ce daya daga cikin 'yan fashin ya tsaya a waje rike da bindiga don tsare mutanen wajen.

Dasuki yayi bayanin cewa sauran biyun sun yi harbi a iska kafin su samu shiga tare da karbar makuden kudaden.

Ya kara da cewa akwai yuwuwar 'yan fashin sun biyo daya daga cikin ma'aikatansu ne da ya je banki don ciro kudin amfanin ofishin.

"Suna shiga ciki suka fara tambayar ina kudi? Ina kudin yake? Sun yi komai a cikin mintocin da basu wuce biyar ba," cewar Manajan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel