Ni da Bichi muka kafa Kwankwasiyya, Kwankwaso butulu ne - Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso

Ni da Bichi muka kafa Kwankwasiyya, Kwankwaso butulu ne - Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana tsohon gwamna kuma tsohon sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin butulu dake yada farfaganda domin cimma burinsa na samun takarar shugaban kasa a 2023 ta kowanne hali.

Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake karbar shugaban jam'iyyar PDP na Kano kuma jigo a tafiiyar Kwankwasiyya, Dakta Rabi'u Suleiman Bichi, tare da dubban magoya bayansa 'yan Kwankwasiyya da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

A cewar Ganduje, "nine kundin sanin Kwankwaso. Babu wanda ya san Kwankwaso fiye da ni. Nine na koya masa siyasa tun kafin shekarar 1999. Kamar yadda mafi yawanku suka sani, nine na samu nasarar lashe zaben fidda dan takarar gwamnan Kano a 1999, amma saboda wasu dalilai aka rarrasheni na zama dan takarar mataimaki.

"Na saka kudina da lokacina wajen yi masa yakin neman zabe a 1999. Na tsaya tare da shi hatta a lokacin da muka fadi zabe a 2003. Amma abun mamaki, Kwankwaso ko sau daya bai halarci yakin neman zabena ba a shekarar 2015 da na fara yin takara, ko sisi bai bani da sunan gudunmawa ba, bai nuna min goyon baya ba kowanne iri."

Ganduje ya bayyana cewa tun lokacin mulkin soja suke tare da Kwankwaso, kuma bai taba butulce masa.

"Tun da nake a rayuwata ban taba ganin dan siyasa mai son kansa kamar Kwankwaso ba. Halayyarsa ce kullum ya cusa wa mutane ra'ayi da bukatunsa, shi kadai kuma, bai damu da naku bukatun da muradu ba.

"Ni da Rabi'u Suleiman Bichi muka kafa darikar Kwankwasiyya wacce yanzu ta rushe tun da Rabi'u Bichi ya fita daga cikinta. Yau mun cire wa Kwankwasiyya zuciyarta," a cewar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel