Kungiyar Shi'a tayi magana a kan jita-jitar mutuwar Zakzaky

Kungiyar Shi'a tayi magana a kan jita-jitar mutuwar Zakzaky

Kungiyar musulmai mabiya akidar Shi'a (IMN) ta yi martani a kan jita-jitan da ke yaduwa na mutuwar shugaban kungiyar, Shekh Ibrahim El-Zakzaky.

A wata takarda da shafin kungiyar ta fitar, mai magana da yawun kungiyar, Ibrahim Musa ya bukaci jama'a da su yi watsi da wannan zancen.

Takardar ce kamar haka "Akasin jita-jitan da ke yaduwa kan shugaban IMN na Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya mutu. Muna son jawo hankulan jama'a da cewa wannan zantukan basu da tushe balle makama don haka a yi watsi dasu."

A yayin kira ga gwamnati don ta sakesa, kungiyar ta bayyana cewa lafiyarsa na kara tabarbarewa ne yayin da yake garkame.

DUBA WANNAN: Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula

"Tun bayan da aka mayar dashi gidan gyaran hali na Kaduna, bai samu damar ganin likita ba duk da kuwa rashin lafiyarsa na kara ta'azzara.

"A don haka ne muke kira ga kasashen ketare da su kara matsantawa gwamnatin Najeriya a kan bukatar barinsa ya ga likita don duba lafiyarsa sannan kuma a sakesa," in ji shi.

Idan zamu tuna, rundunar 'yan sandan birnin tarayya a ranar Talata ta ce kungiyar IMN din ta hari wasu jami'an tsaro da fararen hula a Abuja.

Wannan na kunshe ne a takardar da DSP Anjuguri Manzah, kakakin rundunar 'yan sandan ya fitar.

'Yan sandan sun bayyana cewa 'yan kungiyar a ranar talata sun hari mutane a wajen shataletalen Berger da ke Abuja da kuma miyagun makamai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel