A karon farko: Dasuki ya gurfana gaban kotu bayan sakinsa

A karon farko: Dasuki ya gurfana gaban kotu bayan sakinsa

- Bayan shekarun da Sambo Dasuki ya shafe a tsare, a yau Alhamis ya bayyana a gaban kotu

- Ya gurfana ne a gaban Mai shari'a Ahmed Mohammed na babban kotun tarayya da ke Abuja

- Idan zamu tuna na sako Dasuki ne a cikin watan Disamba baya ya yi shekaru a garkame

A ranar Alhamis ne tsohon mai ba wa shugaban kasa shawara a kan tsaro, Sambo Dasuki ya yi bayyana a gaban kotu bayan shekarun da ya dauka yana garkame.

Ya bayyana ne a gaban Mai shari'a Ahmed Mohammed na babban kotun tarayya da ke Abuja don ci gaban shari'ar zarginsa da ake da almundahanar wassu kudade da aka ware don makamai a 2015.

A cikin watan Disamba ne aka sako Sambo Dasuki bayan shekarun da ya dauka a tsare.

DUBA WANNAN: Sokoto: Hukuncin kotun koli ba zai rage mu da komai ba - Wamakko Read

Ministan Shari’a, Alhaji Abubakar Malami ya ce jin kai da biyayya ga umarnin kotu ne dalilan da suka sa gwamnati ta saki tsohon Mai Bada Shawara ta Fuskar Tsaro Kanar Sambo Dasuki.

A cikin watan Disamba ne gwamnati ta saki Sambo Dasuki bayan shafe sama da shekara hudu a tsare bisa zargin cin hanci da rashawa da karkatar da kudin sayen makamai domin yaki da Boko Haram.

Kafin sakin Sambo Dasuki da Omoyele Sowore gwamnatin ta ja kunnen mutanen biyu da su kame daga aikata abubuwan da za su janyo tayar da zaune tsaye da kuma cikas ga tsaron kasa sannan kuma ka da su yi tarnaki ga shari'ar da ake yi musu bisa dokokin kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel