Abun da Abba Gida - Gida ya fada a kan Kwankwaso bayan ficewar wasu shugabannin Kwankwasiyya

Abun da Abba Gida - Gida ya fada a kan Kwankwaso bayan ficewar wasu shugabannin Kwankwasiyya

Bayan ficewar shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano, Injiniya Rabi'u Suleiman Bichi, mabiya darikar Kwankwasiyya sun mayar da martani kala-kala.

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a zaben ranar 9 ga watan maris na 2019, Abba Kabir Yusuf ya yi martani a kan hakan.

Kamar yadda kungiyar goyon bayan Abba Kabir Yusuf ta wallafa a shafinta na tuwita, ta wallafa hoton Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da wasu kalamai masu nuna iya rintsi ko tsanani suna tare da shi. SHi ne shugaban tafiya kuma umarninsa ne zasu kiyaye.

Kungiyar ta kara da cewa duk wanda ke da burin barin sansaninsu, kada ya ji tsoron yin hakan. Zasu cigaba da jaddada biyayyarsu garesa saboda shi ne bangaonsu.

"Shi ne shugaban kungiyarmu kuma akalar tafiyarmu. Umarninsa sune abin kiyayewarmu. Duk wanda ya ga damar barin tafiyarmu, yana da damar yin hakan. Zamu ci gaba da jaddada biyayyarmu garesa. Shi ne bangonmu," cewar Abba Kabir Yusuf.

Idan zamu tuna, A daren Laraba ne Gwamna Abdullahi Umar ganduje ya karba shugaban jam'iyyar PDP na darikar Kwankwasiyya na jihar Kano, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

A yayin ziyarar da suka kai gidan gwamnatin jihar, Gwamna Ganduje ya karbesa tare da sauran shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomi 44 na jihar. Wannan na kunshe ne a takardar da sakataren yada labarai na Gwamnan, Abba Anwar ya fitar kuma jaridar Solacebase ta samu.

Takaradar ta ce tsohon mai bada shawara na musamman ga Injinay Rabiu Kwankwaso, wasu dalibai da gwamnatin Kwankwaso ta dau nauyin karatunsu, shugabannin jam'iyyu na matakai daban-daban duk sun samu halartar taron da aka yi a gidan gwamnatin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel