Aljannar duniya: Hotunan katafaren gidan biliyoyi da Dino Melaye ya siya a Abuja

Aljannar duniya: Hotunan katafaren gidan biliyoyi da Dino Melaye ya siya a Abuja

- Sannanen abu ne cewa tsohon sanata Dino Melaye na son rayuwa mai cike da jin dadi

- Tun daga kan motocin da yake hawa da kuma irin gidan da yake zama a ciki abin kallo ne

- A cikin kwanakin nan ne sanatan ya siya wani tamfatsetsen gida a garin Abuja wanda ya jawo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita

Tsohon Sanatan Najeriya, Dino Melaye ya siya wani katon gida na biyoyin naira a Abuja.

Sanatan wanda ya saba da kafofin sada zumuntar zamani ya wallafa hotunan tangamemen gidan a shafinsa na Instagram.

Ajannar duniya: Hotunan katafaren gidan biliyoyi da Dino Melaye ya siya a Abuja
Ajannar duniya: Hotunan katafaren gidan biliyoyi da Dino Melaye ya siya a Abuja
Asali: Twitter

Kamar yadda ya rubuta a kasan hotunan, "kada ku tambayeni ta yaya. Ku tambayi Ubangiji da ya dafa min. Ina matukar godiya... Dino Melaye na godiya gareka a kodayaushe. A yau ina kara gode maka don jin kan ka na da tarin yawa."

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe asurgumin dan bindiga, Yunusa Boka, da ya addabi kananan hukumomi 2 a Katsina

Ajannar duniya: Hotunan katafaren gidan biliyoyi da Dino Melaye ya siya a Abuja
Ajannar duniya: Hotunan katafaren gidan biliyoyi da Dino Melaye ya siya a Abuja
Asali: Twitter

Mutane da dama sun taya sanatan murna ta hanyar tura sakonni. Amma kuma wasu 'yan Najeriyan sun caccakesa tare da bayyana cewa dukiyarsu ce yake waddaka da ita.

Mutane da yawa sun zolayi sanatan ta hanyar ce masa "dukiyar mu kuwa tayi maka kyau sosai".

Ajannar duniya: Hotunan katafaren gidan biliyoyi da Dino Melaye ya siya a Abuja
Ajannar duniya: Hotunan katafaren gidan biliyoyi da Dino Melaye ya siya a Abuja
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel