Matar aure ta yi wa mai jego duka bayan ta kama ta a Otel da mijinta

Matar aure ta yi wa mai jego duka bayan ta kama ta a Otel da mijinta

- Dubun wata mata mai shayarwa ya cika bayan da aka kama wani mutum a kanta a dakin otel suna lalata

- Ednah dai ta sha duka hannun matar mutumin wacce kuma kawarta ce sannan makwabciya

- Mai jegon ta kasa boye kwadayinta ne ta yadda har ta nemi mijin kawa kuma makwabciyarta don su yi lalata bayan karamin goyon da ta ke da shi

Wasu abubuwa masu kama da almara na faruwa a Najeriya, duk da halin da kasar nan ke ciki har wasu na da karfin fada da abokan zamansu.

Wata mata mai suna Ednah ta auri Goodluck daga Azuzuama na karamar hukumar Ijaw ta Kudu a jihar Bayelsa.

Kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito, Ednah na shayarwa ne kuma bata kai watanni biyar da haihuwa ba.

KU KARANTA: Kamar karya: Maza kala-kala matata ke kaiwa gadonmu na sunnah - Miji ya koka

Ednah ta je wani otel a Yenagoa don lalata da mijin wata mata kamar yadda bidiyon ya bayyana. Matar mutumin ta yi tattaki inda ta kama mijinta a kan Ednah Goodluck wacce ashe makwabciyarta ce.

A take kuwa aka fara tashin hankali da fada mai tsanani tsakanin matan. Bincike ya nuna cewa Ednah kawar matar ce wacce ta kasa boye kwadayinta har ta kai ga kwantawa da mijinta.

Kamar yadda wacce ta wallafa bidiyon ta wallafa, "wannan mata da kuke gani mai suna Ednah tana da miji mai suna Goodluck. Ta haihu watanni biyar da suka gabata. Ta je otel ne don lalata da mijin wata amma sai matar shi ta kama su. Abun kunyan kuwa shine kawar Ednah ce kuma makwabciyarta ce. Wannan abun ya faru ne a Yenagoa. Idan kai namiji ne me zaka yi wa matarka da ta kwashi karamin dan ka har otel don lalata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel