To fah: Mazan Amurka suma sunce baza ayi babu su ba, yayin da wani Dan Amurka ya zo auren matar shi a Najeriya

To fah: Mazan Amurka suma sunce baza ayi babu su ba, yayin da wani Dan Amurka ya zo auren matar shi a Najeriya

- Wata budurwar Najeriya mai suna Precious Destiny ta zama amaryar wani bature daga kasar Amurka

- Ta bayyana cewa sun fara hira ne a yanar gizo kuma sun dau shekaru uku suna soyayya kafin daga baya ya iso Najeriya

- Ta nuna godiyarta ga Ubangiji tare da fatan ya basu zaman lafiya mai dorewa

Wata budurwar Najeriya mai suna Precious Destiny Stewart ta zama tauraruwa kuma sha kallo bayan da wani masoyinta dan kasar Amurka mai suna Richard Stewart ya garzayo har Najeriya don aurensu.

To fah: Mazan Amurka suma sunce baza ayi babu su ba, yayin da wani Dan Amurka ya zo auren matar shi a Najeriya
Ba Amurke da ya zo Najeriya bikin auren shi
Asali: Twitter

Precious dai 'yar asalin Ukehe ce da ke karamar hukumar Igboetiti a jihar Enugu kuma ta yi bikin kece raini da Richard dan asalin Hawaii da ke Amurka. Ya garzayo takanas ne don auren masoyiyar shi.

A yayin bada labarin tushen soyayyarsu lokacin bikinsu, jaridar YabaLeftOnline ta tattauna da amarya Precious wacce ta ce koda ya fara mata magana a yanar gizo ba ta dau abin da muhimmanci ba.

To fah: Mazan Amurka suma sunce baza ayi babu su ba, yayin da wani Dan Amurka ya zo auren matar shi a Najeriya
Ba Amurke da amaryar shi ana cashewa
Asali: Twitter

Kamar yadda Precious ta ce, ta gama yarda cewa 'yan damfara ne kuwa. Sai ta yanke hukuncin bin ko waye ta yadda ya zo mata. Bayan dogon lokaci ne ya bayyana soyayyar shi gareta kuma ta amince don ta hakika ce.

DUBA WANNAN: Makiyaya guda 4 sun yiwa wasu mata guda 4 fyade a lokaci daya

Precious ta yi bayanin cewa sun yi soyayyar shekaru uku a yanar gizo kafin daga baya ya yanke shawarar zuwa Enugu don bikin auren su.

To fah: Mazan Amurka suma sunce baza ayi babu su ba, yayin da wani Dan Amurka ya zo auren matar shi a Najeriya
'Yar jihar Enugu da angonta dan Amurka
Asali: Twitter

"Mutum ne mara matsala. Ba zan iya godiya ga Ubangiji ba isassa a kan kyautar da ya yi min. Auren shi ne abu mafi muhimmanci da ya faru da ni a rayuwata. Ina fatan Ubangiji ya bamu zaman lafiya mai dorewa, Amen", ta sanar da YabaLeftOnline.

To fah: Mazan Amurka suma sunce baza ayi babu su ba, yayin da wani Dan Amurka ya zo auren matar shi a Najeriya
Amarya da ango
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng