Tir: Da N30, 000 sai ka yi lalata da Matar mutane a Garin Jos

Tir: Da N30, 000 sai ka yi lalata da Matar mutane a Garin Jos

Mun samu labari cewa wani bidiyo da ya nuna yadda Matan aure da ‘Yan mata su ke tafka abin kunya ya zagaye Garin Jos a Jihar Filato.

A wannan bidiyo wanda aka saki faifensa a shafin yanar gizo, an ga mata su na lalata yayin da wani kuma ya ke daukarsu hoto da bidiyo.

A dalilin wannan bidiyo da ya bayyana wajen mutane ne wata daga cikin wanda ta fito a cikin faifen ta kashe kanta saboda tarin bakin ciki.

Daily Trust ta bi diddikin yadda aka dauki wadanan bidiyo na batsa inda ta gano cewa an biya matan kudi ne domin su yi wannan aiki.

Jaridar ta bayyana cewa Matan da su ka yi wannan badala sun samu N30, 000 yayin da aka yi masu alkawarin N10, 000 kuma daga baya.

KU KARANTA: Miyagu sun bi Jagoran APC gida sun bindige har lahira da rana tsaka

Wani mutumi mai suna Emeka da ke zaune a Unguwar Rayfield a Jos, shi ne duk ya shirya wannan aiki a wani otel a Garin Jos da ke Filato.

Wannan Mutumi mai suna Emeka, ya kan biya Dillalan da ke kawo masa wannan mata N10, 000. An yi shekaru ana daukar wadannan bidiyo.

Emeka ya yi wa mutane alkawarin cewa ba za a fito da wannan bidiyo a Najeriya ba. Amma ya saba wannan alkawari, ya wallafa su a nan.

Jim kadan bayan an wallafa wadannan faifai na batsa a wasu shafukan Najeriya, sai Garin Jos ya rude bayan an gane wasu Matan da ke ciki.

Kawo yanzu an cire bidiyoyin, amma an riga an yi ta’adi. Mun ji cewa wani Fasto ya na kokarin dawo da masu wannan aiki zuwa kan hanya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel