Yaki da fasa kauri: Hukumar kwastam ta kama kaya na miliyoyin nairori a jahar Kano
Jami’an hukumar kwastam dake kula da shiyyar Jigawa da jahar Kano sun kama wasu haramtattun kaya da aka yi fasa kaurinsu zuwa cikin Najeriya a sassa daban daban na jahar Kano wanda darajarsu ta haura naira miliyan 80.
Daily Trust ta ruwaito daga cikin wadannan haramtattun kaya da hukumar ta kama a jahar Kano akwai jaka 8,407 na maganin sauro marasa kyau da aka biya masa kudin fito daya kai naira miliyan 54 wanda suka kama a wani katafaren dakin ajiyan kaya dake kauyen Sarauniya.
KU KARANTA: Yan Najeriya sun yi raddi ga Dino Melaye bisa yadda yake gadara da ‘arzikinsu’
Haka zalika hukumar ta kama kwali 8,711 na nikakken tumatir dan kasar waje da darajarsu ta kai naira miliyan 33, kamar yadda kwanturolan kwastam na shiryyar, Nasiru Ahmad ya bayyana yayin da yake gabatar da kayayyakin ga yan jaridu.
Kwanturolan yace sun kama kayan ne a ranar 1 ga watan janairu na shekarar 2020, haka nan sun kama mutum daya dake da hannu cikin shigo da kayan, sai dai yace mutumin yana wakiltar wasu kamfanonin kasar China ne dake hada maganin sauron.
A wani labari kuma, an karrama wani hazikin jami’in rundunar Yansandan Najeriya wanda aka tabbatar da nagartarsa da har tasa ya ki karbar cin hancin kudi naira miliyan 6, mai suna Francis Erhabor.
Dansanda Francis, shi ne DPO na Yansandan garin Itam na jahar Akwa Ibom, an taba masa tayin naira miliyan 6 a shekarar 2019 yayin da yake aiki a jahar Edo don a samu daman fasa bututun mai amma ya ki.
Asali ma abokan aikinsa sun tabbatar da cewa Dansanda Francis bai taba nema ko karban cin hanci a bakin aikin ba, wannan tasa kungiyar Accountability Lab tare da hadin gwiwar Luminate, gidauniyar Mac Arthur da gidauniyar Ford suka karrama shi da lambar yabo ta ‘Integrity Icon summit award’
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng