Yan Najeriya sun yi raddi ga Dino Melaye bisa yadda yake gadara da ‘arzikinsu’

Yan Najeriya sun yi raddi ga Dino Melaye bisa yadda yake gadara da ‘arzikinsu’

Yan Najeriya sun yi diran angulu a kan tsohon Sanatan mazabar jahar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye sakamakon yadda yake ma jama’a gadara tare da kwalelen arzikin daya mallaka, arzikin da suka ce nasu ne ya kwasa.

Dino Melaye ya wallafa wasu hotuna a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda aka hange shi zaune a kan wata kujerar alfarma cikin wani katafaren gida, ya yi ma hotunan taken; “Kada ku tambaye ni ta yaya, ku tambayi Allah wanda Ya yi mani nasibi. Allah mai girma, girma naka ne, Dino Melaye na godiya a kullum.”

KU KARANTA: Za mu dawo da Diezani Allison Madueke gida Najeriya don ta fuskanci hukunci – Magu

Yan Najeriya sun yi raddi ga Dino Melaye bisa yadda yake gadara da ‘arzikinsu’
Dino Melaye
Asali: Twitter

Yawancin yan Najeriya da suka yi tsokaci game da wannan hoto sun yi korafi ne, inda suka nuna bacin ransu da yadda yake nuna gadara da isa, sa’annan suka yi kira ga hukumomin yaki da rashawa da su bincike shi.

Wani daga cikin masu korafin cewa yayi cikin gatse: “Kudin na maka kyau, ba dole mu so ka ba.” Wani mai suna Blessed Beyond cewa ta yi: “Shin rayuwar mutanen daka wakilta ya kai kyawun haka?”

Lekan Yusuf yace: “Abin takaicin shi ne wata rana za’a nema duka wannan a rasa.” Shi kuwa IbezimMillion bude bakinsa keda wuya yace: “Yi alfahari abinka, mutane su mutu baka da matsala, duk da talaucin dake cikin kasar nan, amma kana mana gadara da kudinka, kudin da kai da ire irenka kuka sata daga wajen talakawa.”

BashariyaDarma ko cewa ta yi: “Ji neman fada, dama idan talaka yayi arziki ba tare da wahala ba haka yake da alfahari. Mutane nawa ka gani masu dukiya na gaske suna irin wannan gadarar? Gara ma ka Kankan da kan ka.”

A wani labarin kuma, shugaban hukumar yaki da rashawa dayi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana manufarsa na ganin hukumar ta kamo tsohuwar ministar man fetir Diezani Allison Madueke don ganin ta fuskanci hukunci a gida Najeriya.

Madueke wanda ta rike mukamin ministar albarkatun man fetir a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na fama da tuhume tuhumen badakala, handama da babakere, da kum cin hanci da rashawa a kanta, amma zakara ya bata sa’a ta tsere zuwa Ingila.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng