Sabuwar cuta ta bullo a duniya, ta kashe mutane 9 a Amurka kuma ta fara yaduwa sassan duniya

Sabuwar cuta ta bullo a duniya, ta kashe mutane 9 a Amurka kuma ta fara yaduwa sassan duniya

Cibiyar kula da cututtuka masu yadu wa a Najeriya (CDC) ta bayyana cewa ta fara saka ido da daukan matakan kiyaye wa, musamman a filayen saukar jirgin sama, bayan wata sabuwar cuta mai suna 'Corona Virus' ta fara yaduwa zuwa sassan duniya cikin gagga wa.

Shugaban cibiyar, Dakta Chike Ihekweazu, ne ya sanar da hakan ranar Laraba a shafinsa na Tuwita.

Sanarwar Dakta Ihekweazu na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Amurka ta tabbatar da cewa ta samu bullar sabuwar cutar a kasarta, kamar yadda kafar yada labarai ta Aljazeera ta wallafa a ranar Laraba.

Cutar 'Corona Virus' ta samo asali ne daga kasar China, inda ta kashe mutane 9 tare da kama wasu mutane fiye da 400.

Kasar Japan ma ta tabbatar da cewa yanzu haka ta samu rahoton bullar cutar, wacce har yanzu masana kimiyya basu samu wani cikakken bayani a kanta ba balle su gano maganinta.

Sabuwar cuta ta bullo a duniya, ta kashe mutane 9 a Amurka kuma ta fara yaduwa sassan duniya
Kwayar cutar 'Corona Virus'
Asali: Twitter

Masana kimiyya na duniya da yanzu haka suka fara gudanar da bincike a kan kwayar cutar, sun bayyana cewa cutar na yadu wa a tsakanin mutane, amma ta samo asali ne daga dabbobi.

"Zamu kara zage dantse wajen ganin mun kara sauri a kan biciken tushe da hanyoyin yaduwar cutar," a cewar Li Bin, wani mai ilimin kimiyya a kasar China.

DUBA WANNAN: Likitoci biyu, marar lafiya daya sun mutu bayan bullar wata sabuwar cuta a Kano

Ana zargin cewa kwayar cutar ta samo asali ne daga wata kasuwar sayar da abincin da aka sarrafa da dabbobin cikin ruwa dake Wuhan a kasar China.

A ranar 31 ga watan Disamba, 2019, aka sanar da hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) bullar kwayar cutar 'Corona Virus', kuma a ranar Laraba ne WHO din ta sanar da cewa zata yi wani zama na gagga wa domin tattauna wa da niyyar samun mafita a kan sabuwar kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel