PDP na hada makarkashiya da 'yan majalisa domin su tsige ni - Sabon Gwamnan Imo

PDP na hada makarkashiya da 'yan majalisa domin su tsige ni - Sabon Gwamnan Imo

- Sabon gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya koka a kan yadda jam'iyyar PDP ke shirya munakisar tsige shi

- Uzodinma ya ce ya gano hakan ne bayan PDP na shiryawa a sirrance da 'yan majalisar jihar don tsige shi

- A ranar 15 ga watan Janairu ne kotun koli ta tsige Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan Imo tare da maye gurbin shi da Hope Uzodinma

Sabon gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya koka a kan yadda jam'iyyar PDP ke shirin sirri da 'yan majalisar jihar don su tsige shi.

Ya sanar da hakan ne a wata takarda da mai bada shawara na musamman gare shi a kan yada labarai ya fitar a ranar Talata, 21 ga watan Janairu, kamar yadda jaridar Informationnig ta ruwaito.

"Mun san shirin jam'iyyar PDP da take yi a sirrance da 'yan majalisar jihar Imo. Suna tunani tare da tattaro yadda zasu yi don tsigeni daga kujerar gwamnan jihar. Suna shirin yin duk abinda zasu iya, koda kuwa hadawa da karya ne ga mutane," takardar ta ce.

Idan zamu tuna a ranar 15 ga watan Janairu ne kotun kolin Najeriya ta tsige Emeka Ihedioha wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana a matsayin wanda ya ci zaben jihar Imo.

KU KARANTA: Wata mata ta doke fasto, bayan ya bayyana cewa mata masu kiba baza su shiga aljannah ba

Emeka Ihedioha dan takara ne a karkashin jam'iyyar PDP a zaben ranar 9 ga watan Maris na 2019.

Hope Uzodinma ya garzaya kotun sauraron kararrakin zabe ne don rashin aminta da sakamakon zaben. Kotun ta jaddada nasarar Ihedioha inda tayi watsi da karar Uzodinma. Tuni ya sake garzayawa kotun daukaka kara inda a can ma aka kara jaddada hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe.

Uzodinma bai hakura ba don kuwa ya kara tunkarar kotun koli da koken shi, lamarin da ya kawo mishi nasara har aka kwace kujerar tare da ba shi karagar mulkin jihar Imo kacokan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel