Matan Najeriya basu iya soyayya kamar Turawa ba – Isa Suleiman

Matan Najeriya basu iya soyayya kamar Turawa ba – Isa Suleiman

Wani matashi da labarinsa ya yi tashe a kafofin sadarwa a kwanan nan sakamakon isowar budurwasa Janine Sanchez wacce ta kasance Baturiya, Isa Suleiman Panshekara, ya bayyana cewa a yanzu ba zai iya yin soyayya da wata 'yar Najeriya.

Kamar yadda kuka sani, Janine Sanchez mai shekara 46 a duniya ta niki gari tun daga kasar Amurka har zuwa Najeriya domin haduwa da matashin masoyin nata mai shekara 26 bayan ta aminta da shi.

A wata hira da Isa ya yi da shafin BBC ya ce: "A gaskiya matanmu ba su iya soyayya ba, ko dai za ka ga suna da wata bukata ko kuma suna da buri amma idan baturiya ta ce tana sonka, toh tana fadin haka ne daga zuciyarta."

Masoyan dai sun fara haduwa ne ta shafin Instagram a shekarar da ta gabata inda ta kai su ga fara soyayya da junansu, gashi yanzu har ana maganar aure.

KU KARANTA KUMA: An yi ba’a yi ba: Barawo ya sulale daga Kotu a lokacin da Dansanda yake sharbar barci

Isa ya ce iyayensa sun amince ya auri masoyiyar tasa Janine kuma nan da watan Maris za a yi bikinsu inda za su wuce Amurka.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa cibiyar tabbatar da shari'ar Musulunci ta jihar Kano, Hisbah, a ranar Asabar ta gayyaci dattijuwar Ba Amurkiyar da ta garzayo Kano don auren masoyinta, Sulaiman Isa, zuwa ofishinsu don amsa tambayoyi.

Dattijuwar mai shekaru 45 kuma mahaifiyar 'ya'ya biyu, Jeanine Delsky, ta isa Panshekara ne don haduwa da saurayinta Sulaiman wanda suka hadu a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

A yayin tabbatar da gayyatar, wanda jaridar Daily Nigerian ta yi, Isa ya ce sun fara zuwa ofishin Hisbah na Panshekara ne kafin su gangara hedkwatar cibiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel