Turi ya kai bango: Mutanen gari sun yi fito na fito da yan bindiga, sun kashe 5 a Filato
Wasu gungun yan bindiga da suka fitini al’ummar karamar hukumar Kanam da fashi da makami sun gamu da ajalinsu a hannun ayarin fusatattun jama’an gari da suka yi fito na fito dasu ba tare da jin tsoro ba.
Daily Trust ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a kauyen Jami na karamar hukumar Kanam, inda yan fashin suka tsaya a cikin wata motar pijo 406 a kan hanyarsu ta dawowa daga Pankshin inda suka yi fashi.
KU KARANTA: Sarkin Musulmi da shugaban kiristoci za su tattauna kan mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa isarsu garin keda wuya sai jama’an kauyen suka samu labarin cewa mutanen nan yan fashi ne, domin kuwa sun tare wata motar kamfanin taliya kirar Toyota Bus a kan hanyar Wase-Kanam, suka kwace N1.5m.
Nan da nan ba tare da bata lokaci ba jama’an garin suka fusata, inda suka yi musu kawanya, ko kafin su ankara sun dira kansu da duka har sai da suka halakasu duka, sa’annan suka kwace kudin da suka sata da kuma bindigun da suke amfani dasu, inda suka mika ofishin Yansanda dake Dangi.
Sai dai a nasa jawabin, mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Filato, Tern Tyopev ya bayyana cewa mutum daya kawai aka kashe a hargitsin, sa’annan yace sun kama mutane biyu dake da hannu cikin kisan.
A wani labarin kuma, jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Delta sun samu nasarar kama wata gawurtacciyar yar bindiga dake mummunan sana’ar fashi da makami a jahar Delta mai suna Bella Lucky tare da abokan ta’asanta guda biyu.
Jarumin dansanda, CSP Anieteh Eyoh ne ya jagoranci samamen kama Bella a abokanta a kasuwar McLivers dake garin Warri, a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu.
Dama dai Yansanda sun dade suna farautar Bella sakamakon yadda ta addabi al’ummar garin Warri da kewaye da sata, kwace da kuma fashi da makami.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng