Shari’ar zaben gwamna: Har na cire tsammani daga komawa kujerata – Gwamnan Bauchi

Shari’ar zaben gwamna: Har na cire tsammani daga komawa kujerata – Gwamnan Bauchi

Gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya bayyana cewa ya cire rai da komawa kujerarsa gabanin hukuncin kotun koli domin kuwa ya dauka kotun za ta tsige shi kamar yadda ta yi ma tsohon gwamnan jahar Imo, Emeka Ihedioha.

Bala ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru jim kadan bayan yanke hukuncin kotun da ta tabbatar masa da kujerarsa, inda yace jikinsa ya yi sanyi ne bayan ya ga yadda yan adawa ke bayyana kwarin gwiwarsu tun kafin a sanar da hukuncin.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi da shugaban kiristoci za su tattauna kan mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya

“Abin da ya faru a Imo ya tabbatar da shari’a sabanin hankali ne, abin kuma ya taba ni a matsayina na dan jam’iyyar PDP, kuma abokin tsohon gwamnan, abu ne wanda bamu taba tsammani ba, don haka na san ni ma zai iya samu na.

“Gaskiya hakan ya sa min tsoro sosai a karon farko, saboda ganin yadda abokan hamayyarmu suke bugun kirji tare da cin alwashi game da shari’ar, sai nake gani kamar ko suna da wani tabbaci ne daga wani wuri, amma dai na rike Allah.” Inji shi.

A makon da ta gabata ne aka jiyo gwamnan yana zargin wasu mutane suna kokarin yi masa zagon kasa a kotun kolin, sai dai a da misalin karfe 3 na ranar Litinin, 20 ga watan Janairu, Alkalan kotun suka yanke hukuncin da ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen gwamnan jahar.

Idan za’a tuna, a makon da ta gabata ne kotun kolin Najeriya ta yi awon gaba da gwamnan jahar Imo na jam’iyyar PDP, Emeka Ihedioha, sa’annan ta maye gurbinsa da Hope Uzodinma na jam’iyyar PDP wanda ta bayyana shi a matsayin halastaccen gwamnan jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel