An yiwa Lakcara korar kare bayan ya nemi lalata da dalibar shi
- Hukumar makarantar koyar da aikin Jarida ta Najeriya ta kori wani malaminta mai suna Tene John a kan laifin lalata da daliba
- Dalibar ta ce ya matse ta a ofishinshi inda yayi lalata da ita kuma bai kyaleta ba har sai da ta tabbatar mishi da cewa za ta bashi hadin kai nan gaba
- Duk da malamin ya musanta aukuwar lamarin, hukumar makarantar ta ce ba za ta lamunci irin wannan abu ba
An kori wani malami a makarantar koyar da aikin jarida ta Najeriya wacce ta ke jihar Legas a kan laifin neman wata daliba da lalata.
Kamar yadda Jaridar Linda Ikeji ta ruwaito, Tene John malami ne a makarantar koyar da aikin jarida wanda aka kora saboda lalata da wata daliba mai suna Anjola Ogunyemi.
Dalibar ta bayyana cewa an ci zarafinta yayin da ta ke tare da Tene a Ofishinsa. Ogunyemi ta ce malamin ya yi mata tilas har ya kai ga lalata da ita. Hakazalika bai kyaleta ba har sai da tayi mishi alkawarin cewa zai sameta yadda yake so nan gaba.
Duk da cewa malamin ya musanta aukuwar lamarin, hukumar makarantar ta tabbatar da cewa ta kore shi bayan an bincike shi.
Kamar yadda takardar da hukumar ta fitar a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu ta bayyana;
"Kamar yadda wata dalibar mu ta ajin farko a dufuloma mai suna Anjola Ogunyemi ta wallafa a kafar sada zumunta, ta zargi wani malami mai suna Tene John da cin zarafinta ta hanyar lalata da ita.
KU KARANTA: Lokacin da aka sayar dani kullum sai na kwanta da maza 15 daban-daban - Zainab
"Hukumar makarantar ta samu koken Ogunyemi a ranar 19 ga watan Disamba 2019 wacce ita ce ranar hutu. Shugaban makarantar ya kirata don tabbatar mata da cewa ya samu koken, tare da jaddada cewa za a duba.
"Daga nan ne hukumar makarantar ta kafa kwamitin malamai uku wadanda suka bincika lamarin. A ranar 17 ga watan Janairu ne aka gurfanar da wanda yayi laifin tare da wacce aka yi wa.
"Akwai matukar wahala tabbatar da lamarin saboda kowannensu da abinda yake fadi. A don haka ne muka yanke hukuncin sauwakewa Tene John aikin shi.
"A bangaren dalibar wacce bata dade da dawowa makarantar ba bayan dakatar da ita da aka yi na shekara daya saboda shigar banza, muna jan kunnenta da ta kiyaye rantsuwar da tayi a yayin rantsar da ita a makarantar nan. Wannan makaranta ce mai lullube da dokoki."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng