'Yan Shi'a sun sake arangama da 'yan sanda a Abuja

'Yan Shi'a sun sake arangama da 'yan sanda a Abuja

'Yan sanda sun harbe wani mutum da ke wucewa, a jiya Talata yayin da suke harba bindiga tare da bada borkonon tsohuwa domin tartwatsa mambobin kungiyar Islamic Movement in Nigeria a Abuja.

Mutumin da aka harba a kai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito ya mutu nan take a kusa da shataletalen Berger da ke Wuse a Abuja.

An kuma ruwaito cewa wani mutum ya samu raunin bindiga a kafarsa.

Masu zanga-zangar suna tattaki ne daga Utako zuwa Wuse a cigaba da nuna rashin amincewarsu da tsare shugabansu, Sheikh IbrahimEl-Zakzaky da matarsa.

DUBA WANNAN: Kano: Yadda wata matashiya tayi kisan kai saboda wayan salula

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce: "Ka san yadda 'yan sandan ke harba bindiga da borkonon tsohuwa a duk lokacin da suka zo tartwatsa mu."

Mai magana da yawun 'yan sandan Abuja, Anjugri Manzah, cikin wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce Kwamishinan 'yan sanda, Bala Ciroma ya bayar da umurnin a gudanar da bincike dangane da lamarin.

Ya yi ikirarin cewa 'yan Shi'a suna kai wa mutanen da ba su ji sun gani ba da 'yan sanda hari da muggan makamai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel