Yaki da rashawa: Jami’an kwastam za su dinga bayyana kadarorinsu a duk shekara

Yaki da rashawa: Jami’an kwastam za su dinga bayyana kadarorinsu a duk shekara

A kokarinsa na rage matsalar cin hanci da rashawa, shugaban hukumar kwastam, Alhaji Hamid Ali ya umarci jami’an hukumar kwastam da su dinga bayyana adadin kadarorinsu a kowanne shekara daga bana.

Jaridar The Cables ta ruwaito Ali ya sanar da haka ne a ranar Talata, 21 ga watan Janairu yayin da jami’an hukumar da’ar ma’aikata, CCB, suka kai masa ziyara a ofishinsa a karkashin jagorancin shugaban hukumar, Mohammed Isah.

KU KARANTA: Ya debo ruwan dafa kansa: An tsinci gawar wata Soja a dakin saurayinta

“Dokar hukumar kwastam ta bukaci duk jami’an kwastam su bayyana kadarorinsu da dukiyoyinsu a duk shekara saboda irin aikin da muke yi, aiki ne na kudi, don haka dole ne mu zama abin koyi ga sauran jama’a.

“Da cika wannan takarda ne zamu dinga sanya ma jami’anmu ido, zamu tabbata kowanne jami’in kwastam yana bayyana kadarorinsu a duk shekara daga wannan shekara, don haka muna rokonku ku tabbata kun binciki duk wani abu da jami’inmu ya bayyana a matsayin arzikinsa.” Inji shi.

Daga karshe shugaban hukumar kwastam, Hamid Ali yayi kira ga hukumar CCB dasu wayar da kawunan jami’an hukumar CCB game alfanu da muhimmancin bayyana kadarorinsu, tare da bayyana musu yadda ya kamata su cika takardun.

A nasa jawabin, shugaban hukumar CCB, Mohammed Isah ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin su nemi goyon bayan hukumar kwastam domin jami’anta su bayyana kadarorinsu, don a gano wadanda suke rayuwa cikin halaliyarsu ko haramiyarsu.

Haka zalika Isah ya bayyana cewa hukumar CCB da Kwastam suna aiki kafada da kafada domin yaki da rashawa a Najeriya, musamman saboda dukkaninsu suna da ikon gurfanar da mai laifi a gaban kotu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng