Kano: Yadda wata matashiya tayi kisan kai saboda wayan salula

Kano: Yadda wata matashiya tayi kisan kai saboda wayan salula

A ranar Talata ne aka zargi wata matashiya mai suna Tochukwu da kashe saurayi mai suna Solo a jihar Kano. Solo ya hadu da ajalinsa ne a hannun budurwar bayan da ya nemi karbar wata waya da ya zargeta da sacewa.

Kamar yadda ganau ba jiyau ba ya sanar, Solo yayi kokarin karbar wayarsa ne daga hannun Tochukwu wacce ya zarga da satar masa tare da boyeta a gidansu.

An gano cewa a lokacin da Solo ya ci gaba da matsantawa Tochukwu a kan ta bashi wayarsa, ta jawo wata wuka mai tsananin kaifi daga aljihunta wacce ta soka masa a kirji.

A yayin da marigayi Solo yake fama da tsananin radadin suka daga wukar, ya cigaba da matsawa Tochukwu a kan wayar kafin zubar jini ta rinjayesa ya fadi kasa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon Alƙalin kotun kolin Najeriya rasuwa

Bayan da Solo ya fadi kasa matacce, an gano cewa Tochukwu ta hanzarta barin inda abin ya faru tare da wurga wukar a wata kwata da ke anguwar.

Amma kuma wasu fusattatun matasa da ke kan titin Sani Giwa a Sabon Garin Kano sun hanzarta bin wacce ake zargin inda suka cafketa tare da mika wa 'yan sanda.

Bayan wani lokaci, wasu 'yan sanda sun hanzarta isowa inda abin ya faru tare da daukar gawar da ta jika da jini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: