An kashe mutane 3 a rikicin makiyaya da manoma a garin Kogi

An kashe mutane 3 a rikicin makiyaya da manoma a garin Kogi

Rahotanni sun kawo cewa an kasha wasu makiyaya biyu da manomi daya a garin Ofarachi da ke karamar hukumar Igalamela na jihar Kogi. Rununar yan sandan jihar ta tabbatar da lamarin a wani jawabi da ta saki a Lokoja a ranar Litinin, 21 ga watan Janairu.

An tattaro cewa kisan wani manomi, Godwin Egbunu Omale da ake zargin wasu makiyaya da yi a garin Oforachi a ranar Asabar da kuma rade-radin ramuwar gayya a washegarin ranar ya haifar da tashin hankali a fadin garuruwan da ke yankin.

Mazauna yankin sun ce marigayin ya kai wa yan sanda karar barnar da wasu shanaye suka yi a gonarsa sannan aka bukace shi da ya dawo a washegari, 19 ga watan Janairu , don su samu damar ziyartar gonar domin duba yadda lamarin yake.

A cewarsu marigayin ya koma kamar yadda suka amince sannan yan sanda tare da wasu yan’uwansa suka yi masa rakiya zuwa wajen da lamarin ya faru.

“Yayinda suke kokarin gano makiyayan, sai aka kai masa harin bazata sannan aka kashe shi, yayinda sauran mutanen tare da yan sanddan suka ci kafar kare,” Mista Ojodale Usman ya fada ma majiyarmu ta Daily Trust.

Shugaban kabilar Igalamela ta kasa, Mista Isaac Inna ya ce: “sai da aka shafe sama da sa’o’i biyar kafin samun jami’an tsaro a yankin, wanda hakan ya ba masu laifin damar guduwa."

Ya ci gaba da zargin cewa akwai “rahotannin yanke ma wasu hannayensu, kisan wasu da dama da kuma yiwa mata da yara fyade a gonakinsu ba tare da gwamnati ta dauki mataki ba.”

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya yi tattaki zuwa Chadi, ya gana da rundunar kasa da kasa

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, DSP William Aya ya tabbatar da kisan manomin, inda ya ce an tsinci gawawwakin makiyayan biyu da ake zargin an kashe harin ramuwar gayya ne a kogin Ofu kusa da garin Oforachi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel