Lokacin da aka sayar dani kullum sai na kwanta da maza 15 daban-daban - Zainab

Lokacin da aka sayar dani kullum sai na kwanta da maza 15 daban-daban - Zainab

- A halin yanzu safara tare da bautar da yara mata ya zama ruwan dare kuma kullum cigaba yake

- Wata budurwa mai suna Zainab Lawal ta bada labarin yadda aka yaudareta da alkawarin za a samar mata aiki a Turai kuma aka siyar da ita

- Ta ce tana kwanciya da a kalla maza 15 a rana kafin ta iya hada wa uwar dakinta CFA 20,000 a kowanne wuni bayan irin cin zarafin da take fuskanta

Safara tare da bautar da jama’a ya zama ruwan dare a yanzu. Mutane da yawa na tunanin komawa kasashen waje na sa mutum yayi arziki ko da kuwa babu wani aiki takamaimai da yaje yi. Wasu miyagun mutane kuwa kan yi amfani da rashin aikin yin mutane don siyar dasu tare bautarwa.

Wata budurwa mai suna Zainab Lawal ta bayyana masifar da ta fuskanta sakamakon yunkurin tafiya kasar waje da tayi.

Kamar yadda Zainab ta bayyana, tana zaune a Abuja ne tare da kanwar mahaifiyarta inda suke sana’ar gyaran gashin kai. Bukatar kudi mai tsanani ta taso musu ne sakamakon kammala karatu da zata yi. Tun asali kuwa mahaifiyarta da mahaifinta sun rabu sannan mahaifiyarta ta kara yin aure.

Daga nan ne ta hadu da wani mutum da ya ce zai sama mata aiki a kasar turawa inda zata iya samo wannan makuden kudaden ba tare da bata lokaci. Tuni ta amince tare da tattara kayanta don bin shi Turai.

Kamar yadda Zainab ta bayyanawa Jaridar The Nation Online Ng ta ce, “alamar yaudara ta fara bayyana ne lokacin da muka hau motar haya. Na tambaye shi a ina zamu hau jirgin amma sai yace wajen hawa jirgin zamu tafi. Daga nan dai in takaice muku bamu zarce ko ina ba sai Cote D’ivoire. Babu bata lokaci ya hada ni da wata mata wacce ake kira da Madam Beauty.

KU KARANTA: Mun shafe shekaru ina kwanciya da Fasto din cocin mu a kan gadon auren mu - Matar aure na neman shawara

“Bayan kwanaki ta sanar dani cewa ta siye ni a kan CFA miliyan biyu don haka karuwanci zan fara don mayar mata da kudinta. A kowacce rana tana bukatar CFA 20,000 ne. Daga nan kuwa na fara kazamar sana’ar. Kwastomomina kan yi min duka wani lokacin. Wasu kan zo min a buge kuma su yi min duka. Na taba samun wanda ya fasa kwalba tare da suka ta a hannuna.

“A haka sai da na shekara biyu. Ina kwanciya da maza a kalla 15 kafin in hada mata kudinta na rana daya. Ranar kuwa da ban hada ba ko bani da lafiya, ta kan yi min mugun duka kamar baiwa. Bayan cika ta shekaru biyu ne ta kore ni don ta ce kudina ya cika. In nemi yadda zanyi in tafi gida ko in cigaba da sana’ata.

“Daga nan ne na hadu da wata da ta bani matsuguni a gidanta sannan na samu wata kungiyar kare hakkin mata wadanda suka dau nauyin dawo dani gida.” Cewar Zainab Lawal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel