Wata sabuwa: Budurwar Sulaiman ta yi masa raddi game da sabuwar bazawarsa baturiya

Wata sabuwa: Budurwar Sulaiman ta yi masa raddi game da sabuwar bazawarsa baturiya

A yayin da Sulaiman Isah dan shekara 23 ya kamu da shaukin soyayyar bazawarsa Jenine Delsky yar shekara 46 wanda ta yi tattaki tun daga kasar Amurka zuwa unguwar Panshekara a jahar Kano saboda shi, tsohuwar budurwarsa ta bayyana.

Fitaccen dan jaridar nan, Nasiru Salisu Zango ne ya bayar da wannan rahoto a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook, inda ya bayyana sunan tsohuwar budurwar Sulaiman a matsayin Nafisa Tahir.

KU KARANTA: Lamari ya ta’azzara: Duk wanda suka zalunce mu Allah Ya tsine musu albarka – Kwankwaso

Wata sabuwa: Budurwar Sulaiman ta yi masa raddi game da sabuwar bazawarsa baturiya
Nafisa, Sulaiman da Jenine
Asali: Facebook

Majiyar Legit.ng ya bayyana cewa a hirar da yayi da Nafisa bata nuna wata damuwa da labarin soyayyar saurayinta Sulaiman da bazawararsa yar Amurka wanda ya karade shafukan yanar gizo ba, asali ma cewa ta yi “Umma ta gaida Aisha”.

“Abin bai wani dame ni sosai ba, murna ma na yi, ganin cewa na yi yunwa halin kowa ya bayyana, don haka ina godewa Jenine da ta bayyana da wuri har ta kai abin boye ya fito fili.” Inji ta.

Idan za’a tuna a halin da ake ciki a yanzu haka iyayen Sulaiman sun amince da auren dansu da Jenine, bazawara, uwar yara biyu kuma wanda take sana’ar girke girken abinci a jahar California na kasar Amurka.

Sai dai kafin auren, mahaifin ya gindaya ma Jenine sharadin sai sun samu amincewar hukumar tsaro ta sirri, watau DSS, kuma sai ta kawo wani dan uwanta da zai tsaya mata kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar kafin a ayi auren.

Iyayen Sulaiman dai sun sanya watan Maris a matsayin watan da za’a daure ma masoyan biyu aure, kuma da zarar an kammala bikin, Jenine za ta wuce da mijinta zuwa birnin California na kasar Amurka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel