An gano fuskan sabon shugaban ISIS watanni bayan mutuwar Baghdadi

An gano fuskan sabon shugaban ISIS watanni bayan mutuwar Baghdadi

An tabbatar da cewa Amir Mohammed Abdul Rahman al-Mawli al-Salbi ne sabon shugaban kungiyar 'yan ta'adda na Islamic State da aka fi sani da ISIS.

Rahotanni sun bayyana cewa ya zama shugaban kungiyar ne bayan Abu Bakr- al-Baghdadi ya kashe kansa a watan Oktoban 2019. Shugaban 'yan ta'addan ya tarwatsa kansa da bam ne bayan da dakarun Amurka suka ritsa shi tare da 'ya'yans biyu.

Rahotanni daga hukumomin binciken sirri sun bayyana cewa an nada Al-Salbi ya maye gurbin al-Baghdadi ne sa'o'i kadan bayan mutuwarsa.

Yana daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar da ta gabatar da shari'ar musulunci a Iraqi da Syria. Ana ganin yana daya daga cikin masu fada a aji a cikin wadanda suka yi saura a kungiyar ta ISIS.

Al-Salbi wanda ake yi wa inkiya da nom de guerre Haji Abdullah ko kuma Abdullah Qardash haifafan dan garin Tal Afar ne kuma iyayensu Turkawa ne a Iraqi.

DUBA WANNAN: Ku dena kiran mu NEPA idan kuna son wutan lantarki - DisCos

A matsayinsa na mai tsara doka, al-Salbi yana daya daga cikin tsirarun shugabanin da suka bayar da umurinin da rika jefo 'yan luwadi daga bene da kuma jefa mata ko maza da aka samu da aikata zina.

Kafin mutuwar Baghdadi, sashin bincike na Amurka ya yi alkawarin bayar da Dala Amurka miliyan 5 ga duk wanda zai kawo kan Salbi da wasu manyan shugabannin kungiyar biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel