Gwarama: Mata 13 sun kunna rikici a tsakanin mayakan yan ta’adda, da dama sun mutu

Gwarama: Mata 13 sun kunna rikici a tsakanin mayakan yan ta’adda, da dama sun mutu

Anyi musayar wuta mai tsanani tsakanin mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram dake karkashin jagorancin Abubakar Shekau da kuma mayakan ISWAP dake karkashin jagorancin kungiyar ta’addanci ta duniya, watau ISIS.

Kamfanin dillancin labaru ta AFP ce ta bayyana haka kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, wannan musayar wuta yayi sanadiyyar mutuwar yan ta’adda da dama daga bangarorin biyu, tare da jikkata wasu da kuma lalata motocin yaki.

KU KARANTA: PDP na yunkurin kifar da gwamnatin Buhari – sabon gwamnan APC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mayakan Boko Haram a cikin motoci da dama ne suka kai samame wani sansani na ISWAP dake kauyen Sunnawa cikin yankin Abadam a kusa da iyakar kasar Nijar domin kwato wasu yan mata 13 da ISWAP ta kwace daga hannunsu yayin wani hari da ta kai sansanin Boko Haram.

Wasu majiyoyi biyu dake da masaniya game da lamarin sun tabbatar da cewa “Rikicin ya yi tsanani, da dama sun mutu daga dukkanin bangarorin.” Da farko dai mayakan ISWAP ne suka kai ma Boko Haram hari a sansaninus dake Diffa inda suka ci ganimar matan.

Sai Boko Haram ta gano ashe ISWAP ta ajiye matan ne a sansaninsu dake Sunnawa, don haka ta kaddamar da yakin kwatosu, sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon musayar wutar da aka sha, har yanzu matan suna hannun ISWAP.

A shekarar 2016 ne ISWAP ta balle daga karkashin Shekau da taimakon ISIS saboda sun zarge shi da kashe musulmai da fararen hula, don haka suka karkatar da hare harensu ga Sojoji, sai dai a shekarar 2018 aka yi juyin mulki a ISWAP, inda masu tsaurin ra’ayi suka dare madafan iko, kuma tun daga nan sun cigaba da kashe fararen hula da musulmai.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da babu jituwa tsakanin ISWAP da Boko Haram, sakamakon kowanne bangare na ganin daya bangaren a matsayin kafirai, don haka kullum suna cikin kashe kawunansu ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel