PDP na yunkurin kifar da gwamnatin Buhari – sabon gwamnan APC

PDP na yunkurin kifar da gwamnatin Buhari – sabon gwamnan APC

Sabon gwamnan jam’iyyar APC, kuma gwamnan jahar Imo, Hope Uzodinma ya bayyana cewa manufar wadanda suka shirya zanga zangar jam’iyyar PDP a babban birnin tarayya Abuja shi ne su kifar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Punch ta ruwaito Uzodinma ya bayyana haka ne a ranar litinin, 20 ga watan Janairu yayin da yake ganawa da dandanzon yayan jam’iyyar APC yayin da suka gudanar da zanga zangar goyon baya a gare shi zuwa fadar gwamnatin jahar dake Owerri.

KU KARANTA: El-Rufai ya kaddamar da ilimi kyauta a Kaduna daga Firamari har zuwa Sakandari

“Manufar masu sanya bakaken kaya suna zanga zanga a Abuja da sauran kasashen nan da sunan nuna adawa da hukuncin zaben gwamnan jahar Imo shi ne don kifar da gwamnatin shugaban kasa Buhari, domin idan da saboda zaben jahar Imo suke yi ai da sun yi zanga zangar a Imo.

“Burin PDP shi ne kifar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buharu, don haka nake amfani da wannan dama nake kira ga dukkanin hukumomin tsaro da su fara bincike game da taron gangamin da PDP suke kitsawa.

“Ina so ku cigaba da goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buharu, kun san ni ne dan takarar gwamna a zaben 2019, ban kalubalanci zaben a kan tsarin rikici ba, illa dai na kalubalance shi ne a kan INEC ta hana ni kuri’u na a rumfunan zabe 388.

“Kotun koke koken zabe basu fahimci kukanmu ba, kotun daukaka kara ta bamu gaskiya amma na marasa rinjaye, har sai da muka je kotun koli ne ta fahimci kukanmu, kuma ta bamu gaskiya.

“A yanzu ni ne gwamnan jagar Imo, ni ke da iko da fadar gwamnatin jahar Imo. Allah da Ya bani mulkin jahar Imo zai kare ni, ni ke da iko a nan, kuma zan cigaba da goyon bayan shugaban kasan mu tare da masa addu’an samun nasara.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel