El-Rufai ya kaddamar da ilimi kyauta a Kaduna daga Firamari har zuwa Sakandari
Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayar da umarnin fara aiki da tsarin ilimi kyauta a jahar Kaduna tun daga matakin makarantun firamari har zuwa makarantun sakandari daga ranar Litinin, 20 ga watan Janairu.
Jaridar The Cables ta ruwaito babbar sakatariyar ma’aikatan ilimin jahar Kaduna, Phoebe Yayi ce ta bayyana haka cikin wata wasika data aike ma daraktocin ma’aikatan na shiyya shiyya tare da sashin kula da ingancin ilimi a jahar.
KU KARANTA: Dundum! Boko Haram ta lalata wutar lantarkin garin Maiduguri
“Gwamna ya sanar da ilimi kyauta a jahar Kaduna daga firamari zuwa sakandari a lokacin daya gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dokokin jahar, dama a shekarar 2018 gwamnati ta kaddamar da ilimi kyauta ga dalibai mata daga firamari zuwa sakandari.
“Biyo bayan sanarwar da gwamnati ta sha yi a lokutta daban daban na samar da ingantaccen ilimi kyauta a matakin firamari da sakandari a jahar, gwamnati ta bullo da wasu tsare tsare da zasu tabbatar da yiwuwar hakan.
“Da wannan ne nake sanar daku cewa daga shekarar 2020 gwamnati ta haramta karbar kowanne irin kudi daga hannun dalibai gaba daya, don haka ake umartarku da ku dakatar da shuwagabannin makarantun sakandari dake shiyyoyinku dasu tabbata sun daina karbar ko sisi daga hannun dalibai.” Inji ta.
A wani labarin kuma, ministar kula da harkokin mata a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Uwargida Pauline Tallen ta nada guda daga cikin y’ayanta mata, Violet Osunde mukamin babbar mataimakiya ta musamman a ofishinta.
Duk da yake babu wani tabbacin karya doka karara da wannan mataki da minista ta dauka, amma lauyoyi da masana harkar siyasa sun bayyana hakan a matsayin son kai da nuna bambamci.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng