Obasanjo ya bude kamfanin sutura

Obasanjo ya bude kamfanin sutura

Tsohon shugaban kasa, Olusegu Obasanjo, ya bude sabon kamfanin dinka sutura a cikin harabar dakin karatunsa da ya gina a Abeoukuta, babban birnin jihar Ogun.

Da yake jawabi yayin bude kamfanin ranar Asabar, Obasanjo ya bayyana cewa ya bude kamfanin ne bisa hadin gwuiwa da wata 'yar Najeriya, Abisade Adenubi, wacce ke zaune a kasar Ingila.

"Tunanina ne tun farko a samar da masana'antar, amma wannan matashiya, Abisade, ita ce ya kamata a jinjina wa, saboda ba don ita ba, da ba a bude wannan masana'anta ba a yau," a cewar Obasanjo yayin da ya sanar da cewa sunan kamfanin 'Heritage Apparel'.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Obasanjo ya yi kira ga matasa dasu kasance masu koyi da hazaka da juriya irinta Abisade, wacce ya ce da kyar ta shawo kansa har ya amince aka kafa masana'antar a wannan lokacin.

Obasanjo ya bude kamfanin sutura
Obasanjo yayin bude kamfanin sutura
Asali: Twitter

A nata bangaren, Abisade ta bayyana cewa ta yanke zuwa Najeriya domin kafa kamfanin sutura ne bayan ta shafe lokaci mai tsayi tana sana'ar dinka wa da kera kaya a nahiyar Turai da Asia.

DUBA WANNAN: Buhari ya zayyana alheran rufe bodar Najeriya a Landan

"Na yarda cewazamu iya kara karfin tattalin arzikinmu ta hanyar zuna jari da samar wa jama'a aiki. Mutanenmu suna da basira da kwazon aiki, shi yasa muka kafa wannan kamfani domin basu damar nuna basirar da Allah ya basu," a cewarta.

Ta bayyana cewa bayan samar da suturar irin na gargajiya, tana fatan kamfanin 'Heritage Apparel' zai zama sahun gaba wajen dinka kayan wasannin motsa jiki a Najeria.

A karshe, tayi kira ga masana'antu da hukumomi da sauransu da su hada gwuiwa da sabuwar masana'antar sarrafa sutura ta 'Heritage Apparel'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng