Ganduje da Tambuwal: 'An kasa tsaye, an kasa zaune' a Kano da Sokoto saboda jiran hukuncin koli a yau

Ganduje da Tambuwal: 'An kasa tsaye, an kasa zaune' a Kano da Sokoto saboda jiran hukuncin koli a yau

A ranar Alhamis data gabata ne kotun koli ta tsayar da ranar Litinin, 20 ga watan Janairu, domin yanke hukunci a kan karar kalubalantar kujerun gwamnonin jihohin Kano da Sokoto.

A ranar Laraba ne kotun kolin mai alkalai 7 a karkashin jagorancin alkalin alkalai na kasa, Jastis Tanko Mohammed, ta kwace kujerar gwamnan jihar Imo daga hannun Emeka Ihedioha, dan jam'iyyar PDP, tare da mika ta ga Sanata Hope Uzodinma, dan takarar APC da yazo na hudu a zaben kujerar gwamna a cikin shekarar 2019.

Amma, bayan kotun ta zauna ranar Alhamis kuma ta saurari bangaren masu kara da wadanda ake kara a kan zaben kujerun gwamnonin Kano da Sokoto, sai ta tsayar da ranar Litinin, 20 ga wata domin zartar da hukunci.

A jihar Kano, jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna a zaben 2019, Abba Kabir Yusuf, suna kalubalantar nasarar da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya samu.

Abba da PDP sun shigar da kara a gaban kotun koli ne bayan kotun sauraron korafin zabe da kotun dauka kara sun zartar da hukunci bai daya, watau tabbatar wa da Ganduje nasarar da ya samu.

A jihar Sokoto, jam'iyyar APC da dan takararta na kujerar gwamna, Ahmed Aliyu, sun garzaya kotun koli ne domin cigaba da kalubalantar nasara da INEC ta bayyana cewa gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya samu.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 5 a Zamfara, sun bayar da lambarsu ta waya

Tambuwal ya samu nasara a kotun sauraron korafin zabe da kuma kotun daukaka kara.

Sai dai, ganin yadda kotun koli ta kwace kujerar gwamnan Imo duk da ya samu nasara a kotun sauraron korafin zabe da kotun daukaka kara, hakulan masoya da magoya bayan gwamna Ganduje da Tambuwal sun kasa kwanciya.

A yayin da masu goyon bayan Ganduje ke yin taron addu'o'i na musamman a babban dakin karatu dake kan titin Murtala Muhammad, su kuwa masoya Abba suna yin nasu taron addu'o'in ne a ofishin yakin neman zabensa, kamar yadda jaridar Solacebase dake Kano ta rawaito.

Lamarin a jihar Sokoto ya gimama sosai, don Malaman addinin Islama na jihar Sokoto sun hada sallah ta musamman don neman taimakon Allah a hukuncin da kotun koli zata yanke a kan nasarar Aminu Tambuwal da ake kalubalanta a jihar.

Malaman da suka jagoranci addu'o'in sun hada da Malam Tukur Rijiyar-Zaure, Malam Bala Marina, Malam Aliyu Danbaba da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel