Ramin Kura: Ministar Najeriya ta nada diyar cikinta wani babban mukami a ofishinta

Ramin Kura: Ministar Najeriya ta nada diyar cikinta wani babban mukami a ofishinta

Ministar kula da harkokin mata a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Uwargida Pauline Tallen ta nada guda daga cikin y’ayanta mata, Violet Osunde mukamin babbar mataimakiya ta musamman a ofishinta.

Jaridar Premium Times ta ruwaito duk da yake babu wani tabbacin karya doka karara da wannan mataki da minista ta dauka, amma lauyoyi da masana harkar siyasa sun bayyana hakan a matsayin son kai da nuna bambamci.

KU KARANTA: Dan majalisar Kano ya dauki nauyin dalibai 100 don karatu a kasar Sudan da Indiya

Sai dai ita ma Violet ba sabuwar yanka bace, domin kuwa babbar ma’aikaciya ce a hukumar kula da yan fansho ta Najeriya, ta kammala digirinta a shekarar 2010 a jami’ar Plmouth dake Ingila, sa’annan tana da digiri na biyu daga jami’ar Brunel, Landan, ta fara aiki a hukumar fansho a shekarar 2016.

Daga cikin masu sukar wannan nadi akwai kungiyar malaman jami’a, ASUU, lauyoyi da kuma kaakakin jam’iyyar PDP, inda suka bayyana matakin a matsayin a bin tir da Allah wadai. Amma minista Tallen ta tubure tare da kare kanta, inda tace tana da daman daukan duk wanda zai taimaketa wajen gudanar da aikinta.

Jim kadan bayan samun takardar tabbatar da nadin nata, Violet ta gaggauta rubuta ma shugaban hukumar fansho takarda, inda ta nemi a bata hutun shekara hudu daga wajen aikin domin ta samu daman gudanar da aikinta yadda ya kamata a sabon matsayinta.

Shugaban hukumar ASSU, Farfesa Abiodun Ogunyemi ya bayyana cewa wannan shi ne abinda suka dade suna yaki da shi, inda zaka ga da zarar an nada mutum mukamin jami’in gwamnati, sai ya dauko yan uwansa da danginsa na kauye yana basu mukamai.

A nasa bangaren, mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa dama haka gwamnatin Buhari take tafiya tun bayan samuwarta, babu ruwanta da bacin ran yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel