2023: Bayyanar rigunan yakin neman zaben Atiku da rubutun larabci ya haifar da rudani

2023: Bayyanar rigunan yakin neman zaben Atiku da rubutun larabci ya haifar da rudani

Duk da kasancewar shekara guda kenan kacal da kammala zaben shugaban kasa da aka yi a 2019, tuni 'yan siyasa da dama suka fara shiri da nuna alamun suna son yin takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Wasu sun nuna sha'awarsu kai tsaye, wasu kuma sun nuna alamu ne kawai. Wasu daga cikin 'yan siyasar ma sun fara kulle - kulle ta karkashin kasa a kan yadda zasu cimma burinsu na samun takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyunsu a shekarar 2023.

Irin wanna halayya ta maitar son mulki da 'yan siyasar Najeriya ke nuna wa shine yasa ake ganin basu damu da jama'a ba, da zabe kawai suka damu.

A wannan karon, 'yan Najeriya ne suka shiga rudani da cece - kuce bayan bullar rigunan yakin neman zaben tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, dauke da rubutu cikin harshen Larabci.

Atiku ne ya yi jam'iyyar PDP takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019, amma ya sha kaye a hannun shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda ya sake yi wa jam'iyyar APC takara a karo na biyu.

2023: Bayyanar rigunan yakin neman zaben Atiku da rubutun larabci ya haifar da rudani
Rigunan yakin neman zaben Atiku da rubutun larabci
Asali: Twitter

Bayan kammala zaben 2019, wasu mutane sun bayyana cewa wannan shine karo na farko da Atiku zai nemi takarar kujerar shugaban kasa, saboda tsufa ya kama shi.

Sai dai, har yanzu shahada'unsa suna da ra'ayin cewa har yanzu Atiku yana da gudunmawar da zai bawa Najeriya. Hakan ne yasa wani hoton wasu matasa da rigunan yakin neman zaben Atiku a 2023 suka jawo muhawara mai zafi a dandalin sada zumunta.

DUBA WANNAN: An datse wa wani almajiri kai a Beji

Yayin yakin neman zaben shekarar 2019, Atiku ya yi amfani da salon magana wajen nuna manufarsa ta yin takara, inda ake rubuta "mu hadu mu farfado da Najeriya", watau "Let's Get Nigeria Working Again" daTuranci.

Har yanzu Atiku bai ce komai ba dangane da bullar wadannan riguna na yakin neman zabensa masu rubutun Larabci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel