Yan bindiga sun budewa kwamandan Soji wuta a Kaduna

Yan bindiga sun budewa kwamandan Soji wuta a Kaduna

An garzaya da wani babban hafsan Soja, Laftana Kanar RU Mairiga, asibiti bayan wasu yan bindgia sun bude masa wuta a hanyar Kaduna zuwa Zariya. Premium Times ta ruwaito.

An kaiwa Laftanan Kanar RU Mairiga hari ne misalin karfe 11 na daren ranar Talata, 14 ga watan Junairu, 2020.

Harbin yan bindiga ya jikkatashi inda harsasai suka sameshi a hannu da hakarkari.

Laftanan Kanar RU Mairiga ne kwamdandan Nigerian Army Infantry Corps Centre Record Office dake Jaji, Kaduna.

Ofishinsa ke da hakkin zaben Sojojin da za'a tura wurare daban-daban kafin ofishin sakataren Sojin ta tabbatar.

An kwantar da shi a asibitin barikin Sojin 1 Div dake Kaduna inda aka bayyana cewa yana samun sauki.

Da alamun wadanda suka kaiwa Mairiga hari ne suka kaiwa sarkin Potiskum hari.

Akalla mutane 30 suka rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da 100 lokacin da yan bindiga suka budewa motoci wuta a babbar titin Kaduna zuwa Zariya a ranar Talata, 14 ga Junairu.

Hukumar yan sandan jihar, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa yan bindigan sanye da kayan Sojoji sun kai harin ne misalin karfe 11 na dare.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya ce mutane shida kadai aka kashe kuma biyar sun jikkata. Ya tabbatar da cewa an yi awon da wasu amma bai bayyana adadinsu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel