Buhari ya zayyana alheran rufe bodar Najeriya a Landan

Buhari ya zayyana alheran rufe bodar Najeriya a Landan

A ranar Asabar ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rufe iyakokin kasar nan ya zama abin farin ciki ga manoman kasar nan. Rufe iyakokin kasar nan ya rage shigo da amfanin gona tare da makamai.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a taron da yayi da wasu 'yan Najeriya a Ingila. Ya kara musu bayanin cewa za a yi amfani da rufe iyakokin wajen jaddada tsaro da tattalin arzikin kasar nan.

Ya jaddada cewa ba a rufe iyakokin Najeriya ba don a muzgunawa makwabtan kasar nan ba, amma sai dai don a karfafa tsaro da tattalin arzikin kasar nan.

Shugaban kasar ya danganta rufe iyakokin da aka yi da cigaba da aka samu ta fannin abinci a damina uku da suka gabata. Ya kara da cewa, rage farashin taki da gwamnatin tarayya tayi zuwa kashi 50 ya matukar taimakawa.

Shugaban kasar ya jinjinawa 'yan Najeriya da ke kasashen ketare a kan rawar da suke takawa fannoni da dama na kwarewarsu.

DUBA WANNAN: Buhari ya saka baki a kan hukuncin kisa da Saudiyya ta zartar a kan Malamin Islama dan Najeriya

A yayin da shugaban kasar ke bayanin nasarorin da aka samu a bangaren habaka tattalin arziki, yaki da rashawa da kuma samar da tsaro, shugaban kasar ya ce kullum ana karfafa guiwar matasan kasar da su koma gona kuma su cigaba da rayuwa mai tsafta da mutunta kai.

A bangaren tsaro, ya ce "sanannen abu ne cewa sai da tsaro mai inganci za a iya mulki cikin kwanciyar hankali. Hakan kuwa yayi babbar illa ga yankin Arewa maso gabas na kasar nan."

A yayin magana kan yaki da rashawa, shugaban kasar yace rashawa ta yi muguwar illa ga sunan kasar nan da kuma tattalin arzikinta. Gwamnatinsa ta mayar da hankali ne wajen karbo kadarori da kudaden kasar nan da wasu marasa kishin kasa suka wawura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel