Hisbah ta gayyaci 'yar Amurka data zo auren matashi a Kano, ta sha tambayoyi

Hisbah ta gayyaci 'yar Amurka data zo auren matashi a Kano, ta sha tambayoyi

Cibiyar tabbatar da shari'ar Musulunci ta jihar Kano, Hisbah, a ranar Asabar ta gayyaci dattijuwar Ba Amurkiyar da ta garzayo Kano don auren masoyinta, Sulaiman Isa, zuwa ofishinsu don amsa tambayoyi.

Dattijuwar mai shekaru 45 kuma mahaifiyar 'ya'ya biyu, Jeanine Delsky, ta isa Panshekara ne don haduwa da saurayinta Sulaiman wanda suka hadu a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

A yayin tabbatar da gayyatar, wanda jaridar Daily Nigerian ta yi, Isa ya ce sun fara zuwa ofishin Hisbah na Panshekara ne kafin su gangara hedkwatar cibiyar.

"Babu wani abu a kan gayyatar. An bamu shawarwari ne kuma sun ji daga mahaifina. Sun kuma tabbatar tana da niyya mai kyau a kaina. Don haka suka shawarce ni da in rike addinina bayan mun koma Amurka," in ji shi.

DUBA WANNAN: Zan musuluntar da ita: Matashin da 'yar Amurka ta biyo har Kano don soyayya

Masoya biyun sun hadu ne Instagram a shekarar da ta gabata inda suka fara musayar hotuna tare da soyayyar yanar gizo.

Deslky ta ce ta biyo masoyinta ne har Kano saboda soyayyar da take masa. Ta ce tayi soyayya da mutane masu tarin yawa a yanar gizo amma bata samu tamkar Isa ba. Isa gwanin soyayya ne da kula.

Ta ce sun amince zasu yi aure kuma su tarkata zuwa Amurka inda zasu zauna. An sa ranar auren ne zuwa watan Maris na shekarar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel