An kuma: Wata budurwa 'yar asalin kasar Rasha ta shirya angwancewa da masoyinta dan jihar Katsina (Hotuna)

An kuma: Wata budurwa 'yar asalin kasar Rasha ta shirya angwancewa da masoyinta dan jihar Katsina (Hotuna)

Wasu hotuna da ake zargin na wani dan asalin jihar Katsina ne tare da wata budurwa daga kasar Rasha sun jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Facebook. Hotunan dai sun fara yawo ne inda suke bayyana hoton wani saurayi dan Katsina tare da budurwarsa 'yar kasar Rasha wacce zasu angwance.

Kamar yadda jaridar Katsina Post ta bayyana, wadannan hotunan na masoyan sun fara jawo maganganun mutane tare da tsokaci ta kowanne bangare na kafafen sada zumuntar zamanin.

An kuma: Wata budurwa 'yar asalin kasar Rasha ta shirya angwancewa da masoyinta dan jihar Katsina (Hotuna)
An kuma: Wata budurwa 'yar asalin kasar Rasha ta shirya angwancewa da masoyinta dan jihar Katsina (Hotuna)
Asali: Facebook

Wani mai suna Iyal S. Sambo ne ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook inda yake bayyana yake cewa budurwar 'yar asalin kasar Rasha zata auri saurayin daga jihar Katsina. Ya bayyana jajensa ga 'yan matan Najeriya da aka fara zuwa musu fashin mazaje daga kasashen ketare duk kuwa da cewa iyakokin kasar nan rufe suke.

DUBA WANNAN: 2023: Dattijan 'yan siyasar arewa 4 da suka cancanci samun mulkin shugaban kasa

Kamar yadda Iyal S. Sambo ya wallafa, "Wannan saurayin ya samo tasa daga kasar Rasha. Ina tausayawa 'yan matan Najeriya".

Duk da dai jaridar Katsina Post ta kasa tantance wannan ikirarin na Iyal S. Sambo, amma mutane da yawa sun dinga tururuwa zuwa shafinsa don kallo tare da tsokaci a kan wannan hadin.

An kuma: Wata budurwa 'yar asalin kasar Rasha ta shirya angwancewa da masoyinta dan jihar Katsina (Hotuna)
An kuma: Wata budurwa 'yar asalin kasar Rasha ta shirya angwancewa da masoyinta dan jihar Katsina
Asali: Twitter

Wannan al'amari ya bayyana ne kwanaki kadan bayan wata mata mai shekaru 46 daga California a kasar Amurka ta biyo saurayinta mai shekaru 23 har anguwar Panshekara da ke jihar Kano a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel