Zan musuluntar da ita: Matashin da 'yar Amurka ta biyo har Kano don soyayya

Zan musuluntar da ita: Matashin da 'yar Amurka ta biyo har Kano don soyayya

Jeanine Delsky mata ce mai shekaru 45 'yar asalin kasar Amurka wacce ta sauka a Panshekara, wata anguwa a jihar Kano, don auren saurayinta mai shekaru 23 mai suna Suleiman Babayero Isa.

Delsky wacce ke rayuwa a California ta sauka a filin sauka da tashin jiragen sama ne na AMinu Kano a ranar Asabar kuma ta zarce har Panshekara don haduwa da iyayen masoyinta.

Masoyan sun hadu ne a shekarar da ta gabata a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram inda suka fara musayar hotuna da soyayya a yanar gizon.

A wata tattaunawa da jaridar Daily Nigerian tayi da Delsky, tace ta yanke hukuncin biyo saurayinta Kano ne saboda soyayya.

Ta ce tayi soyayya da mutane da yawa a yanar gizo amma Isa yafi su iya soyayya da kula. Mahaifiyar yara biyun ta ce sun amince da yin aure ne kuma ta taho daga Amurka ne da niyyar aurensa.

DUBA WANNAN: Buhari ya saka baki a kan hukuncin kisa da Saudiyya ta zartar a kan Malamin Islama dan Najeriya

A rike da hannun kyakyawan saurayinta, Delsky tace ta gano cikar mafarkinta ne bayan ta hadu da masoyin ran ta.

"Ya tura min sako ta Instagram inda yace min 'Barka dai' amma ban mayar da martani. Saboda nayi mu'amala da 'yan Najeriya 'yan damfara." a wata hira ta daban da tayi da Kano Focus.

"Amma akwai wani dan damfara da ke yi min sako wanda Sulaiman ya gargada da ya nemi aiki ya bar damfara. Sai nace gaskiya wannan nagari ne." in ji ta.

Isa, wanda ya kammala makarantar sakandire, ya ce a shirye yake don bin budurwarsa zuwa Amurka.

Ya ce bai damu da yawan shekarun da ke tsakaninsu ba "sunna ce ta Annabi Muhammad auren macen da ta girmeka nesa ba kusa ba".

Isa mai sana'ar asski ya ce yana da yakinin wata rana Delsky zata Musulunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel