'Yan bindiga sun kai hari Zangon Kataf a jihar Kaduna

'Yan bindiga sun kai hari Zangon Kataf a jihar Kaduna

- Mutane biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai kauyen Gora-Gan da ke Zangon Kataf

- Maharan sun bayyana ne a kan babura kuma sun afkawa matasan dake wasa a filin gada ne da yammacin ranar Juma'a

- Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro yankin kuma tuni zaman lafiya ya dawo

Mutane biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai garin Gora-Gan da ke karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

Shugaban karamar hukumar Elias Manza, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce maharan sun budewa wasu matasa wuta ne a filin wasa na kasuwar garin a yammacin ranar Juma'a.

Manza ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Asabar yadda lamarin ya faru babu tsammani ga 'yan kauyen, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

DUBA WANNAN: Yadda aka damfareni N68.9m - Tsohon minista

"Maharan sun zo ne a kan babura kuma sun bude wa matasan wuta ne yayin da suke wasanninsu. A take suka kashe mata biyu tare da raunata maza biyu. Wadanda suka samu raunin a halin yanzu suna wani asibiti. Abin farin cikin shine yadda zaman lafiya ya dawo yankin," in ji shi.

Shugaban karamar hukumar yace jami'an tsaron a halin yanzu suna yankin kuma an shawarci mutanen yankin da su kwantar da hankulansu.

Ya bukaci mutanen yankin da su gujewa mayar da martani kuma ana cigaba da binciko wadanda suka yi mugun aikin.

Manza yayi kira ga jama'ar yankin da su kasance masu sa'ido kuma su kai rahoton duk wani abin zargi ga jami'an tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel