Innalillahi: Dan babban malamin Musulunci a duniya ya mutu sakamakon harbin bindiga

Innalillahi: Dan babban malamin Musulunci a duniya ya mutu sakamakon harbin bindiga

An harbe Yousuf Deedat, dan babban malamin addinin Musulunci a ranar Laraba a garin Durban da ke kasar Afirka ta Kudu a ranar Laraba. 'Yan sanda sun bayyana cewa an harbi Yousuf Deedat ne a kansa a ranar Laraba, yayin da yake takawa zuwa kotun iyali ta Verulam a farfajiyar Durban tare da matarsa.

Wanda ake zargin ya bude wuta inda ya raunata Deedat a kai. An kwashesa zuwa asibiti don taimakon likitoci yayin da wanda ake zargin ya haye babur kuma ya tsere, kakakin 'yan sandan yankin, Kanal Thembeka Mbele yace.

Babban dan mamacin ya tabbatar da cewa mahaifinsa ya rasu a asibitin St Anne da ke Pietermaritzburg a yammacin ranar Juma'a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Yadda aka damfareni N68.9m - Tsohon minista

Iyalansa da abokansa na gefensa a asibitin lokacin da yace ga garinku, in ji wata takarda. "Iyalansa na mika godiyarsu ga 'yan uwa da abokan arziki. Allah yayi masa rahama," takardar ta kara da cewa. A halin yanzu an kammala shirin birnesa kuma 'yan sanda na neman wanda ake zargin.

Sheikh Ahmed Deedat ya rasu ne a 2005. Sanannen malamin addinin musulunci ne wanda ya dinga zuwa nahiyar Afirka da'awa. An san shi a duniya a matsayin kwararren malami kuma marubucin littafan addinin musulunci. Shine ya kirkiro da Islamic Propagation Centre International wacce ke taimakawa wajen yada Musulunci a duniya.

Yousuf kuwa sanannen mai rajin kare hakkin mutane ne kuma malamin addinin Musulunci a Durban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel