Allahu Akbar: Mutumin da yafi kowa gajarta a duniya ya rasu

Allahu Akbar: Mutumin da yafi kowa gajarta a duniya ya rasu

- Nepal Khagendra Thapa Magar ne mutumin da yafi kowa gajarta a duniya kamar yadda littafin tarihi na Guinness ya bayyana

- A ranar Juma’a ne Khagendra ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya kuma yana da shekaru 28 a duniya

- Khagendra Thapa Magar Trust ta bayyana cewa za a birne gajeran mutumin a Pokhara a ranar Asabar

Nepal Khagendra Thapa Magar ne mutumin da yafi kowa gajarta a duniya. Gajeren mutumin ya koma ga Ubangiji a ranar Juma’a yana da shekaru 28 a duniya.

Magar, wanda aka kwantar a asibitin koyarwa na Manipal dake yankin Pokhara ya mutu ne bayan jinyar da yayi. Ya samu matsalar numfashi ne inda aka bayyana cewa da kyar yake numfashi a daren ranar Juma’ar. Khagendra Thapa Magar ta tabbatar da mutuwar shi.

Kamar yadda ta bayyana, Khagendra ya mutu ne sakamakon cutar lamaoniya tare da wasu cutukan da suka hada da zuciya, matsalar numfashi da kuma rashin wasu sinadarai masu daukar iska a jini.

KU KARANTA: Yadda wani mutumi yake samun kudi ta hanyar yin bacci

Littafin tarihi na duniya ya bayyana cewa Khagendra Thapa Magar ne yafi kowa gajarta a duniya, kamar yadda aka gwada a watan Oktoba 2010. Yana da tsawon santimita 65.08 wanda yayi dai-dai da kafa biyu da digo 41 a yayin da ya cika shekaru 18 a duniya.

Khagendra Thapa Magar Trust ta bayyana cewa za a yi mishi gatar karshe a Pokhara a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel