So gamon jini: Wata mahaifiya ta sallamawa baturiyar Amurka danta don suyi aure a Kano

So gamon jini: Wata mahaifiya ta sallamawa baturiyar Amurka danta don suyi aure a Kano

- Wani saurayi mai zama a unguwar Panshekara dake Kano ya tsinci dami a kala

- Baturiyar kasar California mai shekaru 45 ce ta biyo shi har gidan don suyi aure kuma su koma Amurka tare

- Mahaifiyar Suleiman tace bata da ta cewa kuma tana goyon bayan wannan hadin, ta amince danta ya bi soyayya

Mahaifiyar saurayi Suleiman ta amince dan ta ya bi wata baturiya mai shekaru 45 wacce tsuntsun soyayya ya daukota daga Amurka domin haduwa da masoyinta da suka hadu a kafa sada zumuntar zamani ta Instagram.

Baturiyar birnin California din tazo daga Amurka har unguwar Panshekara dake Kano, domin tabbatar da soyayyar ta ga matashi Suleman mai shekaru 32. Sun hadu ne a kafar sada zumunta zamani ta Instagram ne da matar.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Na yi tafiya a kafa na sa'o'i biyu bayan harin Boko Haram - Sarkin Potiskum

A halin yanzu, daga an kammala shirye-shirye zata saka masoyin nata a gaba su wuce kasar Amurka.

Fatima Suleiman wacce ita ce mahaifiyar saurayi Suleiman, tace bata da suka a kan lamarin. Ta amince danta ya bi masoyiyar tasa zuwa kasar Amurka.

Ango Suleiman kuwa yace shi dama bashi da burin da ya wuce ya haifa yara ruwa biyu masu masifar kyau kalar turawa. Ya kuma yi alkawarin zai dinga kawo ziyara Najeriya don gaisawa da ‘yan uwa da abokan arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel