Hukuncin kotun koli: PDP tayi muhimman tambayoyi 6

Hukuncin kotun koli: PDP tayi muhimman tambayoyi 6

- Har yanzu dai jam’iyyar PDP na ta kokarin fahimtar hikimar shari’ar kotun koli a zaben gwamnoni na jihar Imo

- Jam’iyyar PDP din ta mika wasu muhimman tambayoyi shida ga alkalin alkalan Najeriya, Tanko Muhammad

- Jam’iyyar na gani cewa an yi mata fashin hakkinta ne a kotun kolin ta Najeriya

Har yanzu dai jam’iyyar PDP bata farfado daga hukuncin kotun koli ba ta yadda ta kwace kujerar Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan jihar Imo.

Jam’iyyar PDP ta cigaba da bayyana mamakinta inda ta mika wasu tarin tambayoyi a kan hukuncin da ya tabbatar da Hope Uzidinma na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Imo.

Ga tambayoyin da jam’iyyar PDP ta mika ga kotun kolin:

1. Shin kotun kolin na da damar hada kuri’u tare da bada su ga wanda taso?

2. Shin wadannan kuri’un INEC ta aminta dasu?

3. Ko Hope Uzodinma ya kira shaidu 388 daga akwatuna 388 din ne don su tabbatar da kuri’un da aka kara masa a kotun?

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Na yi tafiya a kafa na sa'o'i biyu bayan harin Boko Haram - Sarkin Potiskum

4. Ina aka bar shugabannin akwatuna da wakilan jam’iyyun a lokacin da aka kara wa Hope Uzodinma kuri’un a kotun kolin?

5. Kuri’u nawa ne aka samu daga kowanne akwati cikin akwatuna 388 din da aka tattara kuri’unsu suka mayar da Uzodinma mai nasara?

6. Kuma a kan mene kotun kolin ta nuna cewa kuri’un akwatuna 388 din duk na APC ne duk da kuwa an samu ‘yan takara sama da 70 dake neman kujerar?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: