Babban hafsan Sojan sama ya fadi matakin da Buhari ya dauka don gamawa da Boko Haram da yan bindiga

Babban hafsan Sojan sama ya fadi matakin da Buhari ya dauka don gamawa da Boko Haram da yan bindiga

A ranar juma’a, 17 ga watan Janairu jim kadan kafin ya wuce kasar Birtaniya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da manyan hafsoshin hukumomin tsaron Najeriya.

Jim kadan bayan kammala taron ne guda daga cikin wadanda suka halarci taron ya shaida ma yan jaridu cewa sun kalli dukkanin lamurran tsaro da idon basira, kuma daga karshe sun gamu da cigaban da ake samu a fannin tsaro.

KU KARANTA: Kara da kiyashi: Yadda wani mutumi ya kashe abokinsa har ya cinye marainansa

Premium Times ta ruwaito shi ma babban hafsan sojan sama, Sadique Abubakar ya bayyana ma manema labaru cewa daga cikin kayan yakin da gwamnati ta mallaka mata, rundunarsa ta sayo sabbin jiragen yaki domin gamawa da Boko Haram da yan bindiga.

“Wasu daga cikin makaman da muka samu sun fara isowa Najeriya, mu dai a rundunar Sojan sama mun samu manyan jiragen yaki guda biyu, kuma sun iso Najeriya a ranar 15 ga watan Janairu, a yanzu haka muna aikin harhadasu ne domin su kara yawan kayan aikin da muke dasu a kasa.” Inji shi.

An dauki tsawon lokaci ana fama da matsalolin tsaro daban daban a duk fadin Najeriya, daga ciki akwai yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabas, yan bindiga a Arewa maso yamma da kuma masu garkuwa da mutane a sassan kasar.

Ko a kwanaki biyu da suka gabata sai da yan bindiga suka bude ma matafiya wuta a kan hanyar Zaria zuwa Kaduna, inda suka kashe akalla mutane 30, sa’annan suka yi awon gaba da wasu mutane 100.

A wani labarin kuma, tsohon shugaban jam’iyyar APC, Cif John Odigie Oyegun ya bayyana cewa tsarin mulkin dimukradiyya ya tabbata a Najeriya, tamkar takalmin kaza, mutu ka raba. Sai dai ya koka kan yadda yan Najeriya basa jin dadin tsarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel