Yanzu Yanzu: Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Landan

Yanzu Yanzu: Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Landan

Jirgin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Landan a yau Juma’a, 17 ga watan Janairu.

Ana sanya ran Shugaban kasar zai halarci taron kasuwanci na Birtaniya da Afrika wanda za a guanar a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu.

Firaye ministar Birtaniya, Boris Johnson ce ta shirya taron, sannan ana sanya ran zai hada shugabannin Afrika, manyan yan kasuwa na kasa da kasa, da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa.

Yanzu Yanzu: Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Landan (hotuna)
Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Landan
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya samu rakiyar Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe dda kuma Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Yayinda zai kasance a Ingila, shugaba Buhari zai gana da Shugaban kungiyar Commonwealth, Prince Charles a Glasgow, Scotland.

Yanzu Yanzu: Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Landan (hotuna)
Shugaba Buhari ya samu rakiyar Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe dda kuma Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gwamna Sule ya yi magana kan Amotekun, ya ce tuni suka fara aiki da kungiyoyin tsaro na sa-kai a Nasarawa

Shugaban kasar da tawagarsa za su gana da Firai minista Johnson da shugabannin wasu kungiyoyi.

Ana sanya ran zai dawo Abuja a ranar Alhamis mai zuwa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da shugabannin tsaro a fadarsa dake Aso Rock a Abuja. An gano cewa ya shiga taron da shugabannin tsaron ne ana sauran sa'o'i kadan ya daga zuwa birnin London.

Rahoton ya nuna cewa, akwai yuwuwar taron ya zama daya daga cikin tarukan da yake yi da shugabannin tsaron kasar nan, inda suke bayyana mishi halin da kasar ke ciki ta fuskar tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel