Gwamnatin tarayya ta bayyana ainahin ranar da za a fara karban karin kudin haraji

Gwamnatin tarayya ta bayyana ainahin ranar da za a fara karban karin kudin haraji

Ministar kudi ta kasa, Zainab Ahmed ta bayyana cewa akanta-janar na kasar, Ahmed Idris ya yi tuntuben harshe da ya ce an fara amsar haraji tun daga ranar Litinin da ta gabata.

A ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu ne Idris ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara karbar haraji na karin 7.5 bisa 100 tun daga ranar Litinin, 13 ga watan Janairu.

A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar kariji wato VAT hannu indda ya tashi daga kashi 5 bisa 100 zuwa kashi 7.5 bisa 100.

Sai gashi a jiya Alhamis Akanta-Janar ya kira taron manema labarai, inda ya bayyana cewa daga ranar Litinin ce za a fara karbar harajin VAT, wanda gwamnatin Buhari ta kara daga kashi 5 zuwa kashi 7.5 daga wasu kayyayakin da ’yan Najeriya ke saye, sayarwa ko wasu huldodin kasuwancin da suka yi.

Yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a ofishin sa, Idris ya yinkarin hasken cewa wannan sabuwar doka duk wasu kudaden da gwamnatin tarayya ta biya daga asusun ta, to za a fara cire kashi 7.5 na haraji nan take.

To amma da ta ke jawabi wajen rantsar da mambobin FIRS, a jiya Alhamis a Abuja, Zainab ta ce sai ranar 1 ga watan Fabrairu sannan dokar karin kudin harajin za ta fara aiki.

Daga nan ta yi kira ga mambobin hukumar gudanarwar FIRS su jajirce wajen tabbatar da cewa hukumar ta cimma kudirin da aka dauka za ta cimma, wato na tattara makudan kudaden harajin da ba na kudaden ribar man fetur ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe hakimi wani kauyen Niger, sun sace mutum 17

Shi ma Shugaban FIRS, Muhammad Nami, ya yi kira ga mambobin su hada kai domin a cimma nasarar da aka tunkara a yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel