Yadda aka damfareni N68.9m - Tsohon minista

Yadda aka damfareni N68.9m - Tsohon minista

Tsohon ministan wuta da karafa, Alhaji Bashir Dalhatu, ya sanar da wata babbar kotun tarayya da ke Zuba yadda aka damfaresa naira miliyan 68.9. Alhaji Bashir Dalhatu ya bayyana ne a gaban kotun a matsayin shaidar mai gabatar da kara wacce EFCC ta mika a kan wani dan kasuwa, Imeh Akpan, a zarginsa da ake da cin amana.

Wazirin Dusten ya bayyana yadda Marigayi Alhaji Aliyu Alkali da Haruna Ningi suka gabatar masa da wanda ake zargin a 2004.

Ya zargi cewa wanda ake zargin ya sanar dashi yadda zai saka hannun jari a masana'antar sufurin jiragen sama, ta hanyar siyan hannun jari a kamfanin da ake tashe a wancan lokacin.

Kamar yadda yace, "ya sanar dani cewa akwai matukar riba a wannan lokacin. Bayan na gamsu, sai na siya hannun jari na naira miliyan 1.8 wanda ke wakiltar kashi 34 na dukkan jarin kamfanin. Ya sanar dani cewa yana fafutukar neman bashi da First Atlantic Bank don kamfaninsa mai suna 'Commodore Aviation Services'."

Tsohon ministan ya sanar da kotun cewa wanda ake zargin yace zai yi amfani da bashin ne don siyan jirgin da kamfanin zai dinga amfani dashi a nan kasar.

DUBA WANNAN: Hotunan ziyarar da Ahmed Musa da 'yan kungiyarsa suka kai wa yariman Saudiyya

Alhaji Bashir Dalhatu ya cigaba da bayyanawa kotun cewa wanda ake zargin ya same shi tare da rokon ko zai samu wata naira miliyan hamsin don samun damar karbar bashin.

Yace, "Na amince da bashi bashin miliyan hamsin din a kan sharudda biyu. Daya daga ciki shine a bude asusun banki wanda za a zuba kudin amma mai kawo riba da sunan 'Commodore Aviation Services. Na biyun kuwa shine zai rike ribar da aka samu bayan watanni shida amma zai dawo min da kudin da na ranta."

Basaraken ya kara da cewa sun amince cewa dashi da wanda ake zargin ba zasu cire kudi daga asusun bankin ba kuma sa hannun mutane biyu za a yi amfani dashi wajen bude asusun bankin.

Yayi bayanin cewa a ranar 28 ga watan Mayu, 2004, an bada jimillar kudin da wannan asusun ya samu a naira miliyan hamsin da takwas.

Alhaji Bashir Dalhatu yace wanda ake zargin ya tunkaresa da cewa ya kara naira miliyan 10.7 don kamfanin jirgin saman ya fara aiki a jamhuriyar Niger.

Ya bayyanawa kotun yadda ya fusata kuma ya bukaci da a bashi kudinshi tare da duk ribar da kudin suka samar.

Ya kara da cewa "daga baya ne na gano cewa kudin basu cikin asusun hadin guiwar. Suna cikin wani na daban ne mai irin wannan sunan kuma wanda ake zargin ne ya mallakesa. Bayan kokarin karbo kudin sun gagara, a watan Janairu na 2013 ne na mika koke na ga EFCC don su binciki wanda ake zargin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel