Gwamna Zulum ya samu lambar yabon Musulmi mafi kokari a Najeriya, Pantami yazo na biyu

Gwamna Zulum ya samu lambar yabon Musulmi mafi kokari a Najeriya, Pantami yazo na biyu

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umarar Zulum, ya samu lambar yabon Musulmi mafi kokari a Najeriya na shekarar 2019, na jaridar Musulmai, Muslim News, jaridar Musulunci ta daya a Najeriya.

Samun lambar yabon Farfesa Zulum bai zo da mamaki ba bisa ga irin bajintar da ya nuna a faggen shugabanci tun lokacin da aka rantsar da shi a watan Mayun 2019.

Duk da kasancewar jihar Borno cikin yaki da Boko Haram, Farfesa Zulum bai yi kasa a gwiwa wajen ganin cewa al'ummarsa sun debi romon demokradiyya ba.

A cewar jaridar, Zulum ya taka rawar gani a bangarori daban-daban irinsu tsaro, ilimi, kiwon lafiya, sufuri, tattalin arziki, da tallafi ga yan sansanin gudun hijra.

Gabanin zama gwamna, Farfesa Zulum ya kasance kwamishanan gine-ginen gidajen da Boko Haram suka lalata karkashin tsohon gwamna, Kashim Shettima.

Ga jerin wadanda suka samu lambar yabon:

1. Farfesa Babagana Umarar Zulum

2. Sheikh Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami (Ministan sadarwa kuma tsohon shugaban hukumar NITDA)

3. Farfesa Is'haq Oloyede (Shugaban hukumar jarabawar JAMB)

4. Farfesa Lakin Akintola

5. Farfesa Fatima Batul Mukhtar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng