Allah Sarki: Dan shekara 14 ya bayyana yadda ya sayar da kodarshi domin ya biyawa kanshi kudin makaranta

Allah Sarki: Dan shekara 14 ya bayyana yadda ya sayar da kodarshi domin ya biyawa kanshi kudin makaranta

- Wani yaro mai shekaru 14 mai suna Wanjala ya tashi hankulan iyaye, 'yan uwa da abokan arziki

- Ya bayyana cewa zai siyar da kodar shi daya don ya samu ya biya kudin makarantar sakandire da jami'a

- Iyayen yaron sun tada hankulansu saboda basu da kudin biya mishi kuma suna tsoron hatsarin dake tattare da siyar da kodar

Isaiah Wanjala yaro ne mai shekaru 14 wanda ya fito daga kauyen Gidea dake mazabar Kwanza, a yankin Trans Nzoia. An zabe shi don cigaba da karatu a babbar makarantar yara maza dake Chewoiyet.

Ya samu maki 394 a 2019 a jarabawar kammala firamare. Mazauna kauyen da iyayen yaron sun firgita bayan da yace a shirye yake don siyar da kodar shi don biyan kudin makarantar sakandirenshi.

Iyayen shi sun kasa hada Sh50,000 wanda za a biya kudin makaranta a yammacin Pokot.

"Tsoffin iyayena basu da halin hadamin kudin makaranta tare da samar da abubuwan bukata garemu," cewar Wanjala.

KU KARANTA: Budurwa ta bayyana yadda ta sayar da budurcinta kan kudi Naira miliyan 473 a yanar gizo

Da aka tambayeshi yadda zai cire kodar, Wanjala yace a shirye yake ayi mishi tiyata don cire daya daga cikin kodojinshi matukar zai samu kudin makaranta.

Amma iyayenshi, Rose Andisi da Fred Wanyoyi sun tashi hankulansu tun bayan da yaron ya sanar dasu niyyar shi.

Yaron ne na biyar a cikin yara tara da ma'auratan suka haifa.

Iyayen sun bazama nemawa dan su taimakon jama'a don samun cikar burin shi na zama Injiniya.

"A matsayinmu na iyayen shi, munyi matukar damuwa a kan hukuncin yaron. Munyi kokarin hana shi amma yaki hanuwa kuma yace sai ya cika burin shi," inji iyayen shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel