Mijina da yayi mini ciki sai ya gudu, baya dawowa har sai yaji cewa na haihu - Rukayya

Mijina da yayi mini ciki sai ya gudu, baya dawowa har sai yaji cewa na haihu - Rukayya

- Wata mahaifiyar yara uku ta gurfana a gaban kotu da rokon a tsinke igiyar aurensu da mijinta

- Tace mijinta mai duka ne kuma mashayi ne wanda ke guduwa ya barta matukar ta samu juna biyu

- Ya kan bata N200 a matsayin kudin cefane amma idan tayi korafi sai yayi mata mugun duka tare da zagin iyayenta

Wata mahaifiyar yara uku mai suna Rukayat Sanusi ta roki wata kotu dake Mapo a ranar Alhamis a kan ta tsinke igiyoyin auren ta da mijinta.

A yayin mika shari'ar gaban alkali Ademola Odunade, Rukayat wacce take zama a yankin Tuntun dake Ibadan ta ce mijinta mashayi ne, mai dukan mace kuma baya daukar dawainiyarta.

Kamar yadda Rukayat tace, mijinta ya karo aure ne a lokacin da yaronsu na farko ke da watanni biyu tak.

"Ya saba guduwa in har ina da ciki amma sai ya dawo idan na haihu. A takaice N200 yake bani a kudin cefane amma duk lokacin da nayi korafin kankantar kudin, sai ya zaneni.

"A lokacin da na kasa jure dukan, na tsere zuwa gidanmu don ceton raina. Amma yana zuwa don zagi tare da barazana ga 'yan uwana," tace.

KU KARANTA: Bincike: An gano cewa akwai maganin cutar daji a jikin dabino

Rukayat ta ce shekaru takwas kenan da ta bar gidan mijinta don zama da iyayenta.

"A lokacin da mahaifiyata da 'yar uwata suka roke shi, ya zagesu tatas tare da alkawarin cin mutuncin duk namijin da ya gani tare dani," tace.

Lanrewaju, wanda ya amince da sakin yace duk sharri ake mishi.

Yace dangin matar shi ne basu son shi kuma ya kwace dan shi ne don yaron na korafin cewa mahaifiyar saurayin maman shi na dukan shi.

Bayan sauraron kowanne bangare, Odunade ya tsinke igiyar aurensu don tabbatar da zaman lafiya. Ya umarci mahaifiyar da ta kwashe yaran don kula dasu. Ya kara da umartar Lanrewaju da ya dinga biyan N15,000 na ciyar da yaran duk wata kuma ya dau sauran dawainiyarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel