Kau da bara: Limamai sun yi wa Tambuwal addu'o'in samun nasara a kotun koli (Hotuna)
Malaman addinin Islama na jihar Sokoto sun hada sallah ta musamman don neman taimakon Allah a hukuncin da kotun koli zata yanke a kan nasarar Aminu Tambuwal da ake kalubalanta a jihar.
Idan zamu tuna, kotun kolin ta saka ranar 20 ga watan Janairu don jin hukuncin karshe na zaben 9 ga watan Maris na jihohin Kano, Sokoto, Benuwe, Filato da Adamawa.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa malaman sun hadu ne a babban masallacin idin jihar don yin addu'o'i. Malaman da suka jagoranci addu'o'in sun hada da Malam Tukur Rijiyar-Zaure, Malam Bala Marina, Malam Aliyu Danbaba da sauransu.

Asali: Facebook
Wasu malaman da suka samu zantawa da manema labarai sun bayyana cewa matukar aka hana jama'ar jihar bukatarsu, suna tsoron zata yuwu zaman lafiya a jihar yayi kaura.
Kamar yadda suka tabbatar, zuwan Tambuwal a matsayin gwamnan jihar ya taimaka wajen fatattakar wasu kalubalen da jihar ke fuskanta wadanda suka hada da luwadi, ta'ammali da miyagun kwayoyi, daba da sauransu.

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng