Buhari ya nada sabon mataimakin gwamnan CBN

Buhari ya nada sabon mataimakin gwamnan CBN

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya zabi Dakta Kingsley Obiora a matsayin sabon mataimakin gwamnan babban bankin kasa (CBN), kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta bayyana a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar, tuni shugaba Buhari ya aike da sunan Dakta Obiora zuwa majalisar dattijai domin tabbatar da shi.

"Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aike da suna Dakta Kingsley Isitua Obiora zuwa majalisar dattijai domin tabbatar da shi a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya.

"A cikin wasikar da ya aika wa shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, Buhari ya bayyana cewa ya zabi Obiora ne bisa dogaro da sashe na 8(1) (2) na babban bankin Najeriya da aka zartar a shekarar 2007.

Buhari ya nada sabon mataimakin gwamnan CBN
Buhari
Asali: UGC

"Dakta Obiora, idan majalisa ta tabbatar da shi, zai maye gurbin Dakta Joseph Nnanna, wanda zai yi ritaya a ranar 2 ga watan Fabarairu, 2020," a cewar sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa, Femi Adesina.

DUBA WANNAN: Abubuwa 5 da suka fi jan hankalin mata a tattare da namiji

Dakta Obiora yana da shaidar karatun kammala digiri na farko a fannin tattalin arziki daga jam'iar Benin, digiri na biyu fannin daga jami'ar Ibadan, da kuma digiri na uku a fannin kudi da tattalin arzikin kasa da kasa daga jami'ar Ibadan.

Yanzu haka ma'aikaci ne a wata hukumar harkokin kudi ta kasa da kasa dake birnin Washington a kasar Amurka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel